Rufe kan iyakoki alheri ne ga Najeriya – Shugaban Kwastan

0

Shugaban Hukumar Kwastan ta Kasa, Hamid Ali, ya bayyana cewa rufe kan iyakokin Najeriya alheri ne mai dimbin yawa ga Najeriya.

Da ya ke bayani yau a Abuja, Ali ya ce harajin da Najeriya ke samu sakamakon rufe kan iyakoki ya karu matuka, fiye da lokacin da kan iyakoki ke bude.

Sai ya kara da cewa farkon rufe kan iyakoki gwamnati ta rika fargaban kada kudaden shiga su ragu. Amma maimakon raguwa, sai ma karuwa kudaden shigar su ka yi.

Shugaban na kwastan ta ce a yanzu kudaden shigar da Najeriya ke samu karuwa ma suke bayan rufe kan iyaka, fiye da lokacin da iyakokin ke a bude.

“Akwai ranar da muka tara sama da naira biliyan 10 a rana daya. Daga nan aka rika tara fiye da biliyan 4 da kuma sama da biyan 5 a rana daya. Don haka idan za a ci gaba da karin samun kudin shiga idan kan iyaka na rufe, to babu wata damuwa don ta ci gaba da kasancewa a rufe.

“Wato kafin mu rufe iyakoki, jiragen ruwa sai su rika karkatawa Kwatano su na sauke kaya. Daga nan a yi sumogal din su cikin Najeriya.

“Amma a yanzu da aka rufe kan iyaka, tilas wadannan jiragen ruwa su na zuwa tashar ruwa da Apapa da Tin Can su na sauke kaya, kuma ana biyan haraji kafin mai kaya ya dauka.”

Da ya koma kan masu sumogal din fetur daga Najeriya. Ali ya ce an gano a kullum ana fitar da fetur lita milyan 10.2 wajen kasar nan ta kan iyakoki ta sumogal.

Share.

game da Author