Hukumar Kwastan ta kasa (NCS) ta bayyana cewa ta kama motoci 1,072 da wasu kayayyaki da gwamnati ta hana shigowa da su daga ‘yan sumogal a jihar Katsina.
Hukumar ta kama wadannan motoci da kaya ne a daidai ‘yan sumogal na kokarin shigo da su kasar nan ta barauniyar hanya dake iyakan kasa a jihar.
Kakakin hukumar Joseph Attah ya fadi haka ranar Juma’a a garin Katsina a taron inganta rufe iyakokin kasa da hukumar ta yi a jihar.
Attah yace an Kama buhunan shinkafa 19,000,jarkokin fetur 4,765, tankunan Mai, bindigogi da dama,buhunan takin zamani NPK 131,mutane wadanda ba ‘yan Najeriya ba 146 da mutane 317 da ke da hannu a shigo da wadannan kaya kasar nan.
Ya ce gwamnati ta rufe iyakokin kasar nan ne domin hana aiyukkan ‘yan sumogal da shigowar mutanen da ba ‘yan Najeriya ba.
“A yanzu haka wannan tsari ya taimaka wajen inganta tsaro da bunkasa tattalin arzikin kasa Najeriya.
Attah ya yi kira ga mutane da su guji siyan kayan da ‘yan sumogal suka shigo da su Yana Mai cewa yin haka na gurguntar da tattalin arzikin kasan.
Idan ba a manta ba a ranar Talata ne Shugaban Hukumar Kwastan, Hamid Ali, ya bayyana cewa rufe kan iyakokin Najeriya alheri ne mai dimbin yawa ga Najeriya.
Ali ya ce harajin da Najeriya ke samu sakamakon rufe kan iyakoki ya karu matuka, fiye da lokacin da kan iyakoki ke bude.
Sai ya kara da cewa farkon rufe kan iyakoki gwamnati ta rika fargaban kada kudaden shiga su ragu. Amma maimakon raguwa, sai ma karuwa kudaden shigar su ka yi