Tun daga watanni biyu bayan rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari, sabuwar gwamnatin sa da aka yi wa lakabi da ‘Next Level’ ta ke ta bijiro da wasu hanyoyin da ta ke ganin su ne mafita wajen inganta tattalin arzikin kasar nan.
Sai dai kuma da dama na ganin wadannan hanyoyi duk sun yi tsauri sosai, kuma duk ya yadda za a yi dai takala ne mai shan wahala a karshe.
Tun kafin hawan Buhari a 2015, alkawarin sa shi ne talaka zai samu saukin rayuwa fiye da zamanin mulkin PDP idan ya hau mulki.
Kash, sai dai kuma da yawa na samu saukin da aka yi tunani za a samu daga 2015 ba. Sannan kuma a yanzu a zango na biyu, an shiga Nes Labul ana ya bijiro da tsare-tsare da talaka ke ganin an sa kuncin rayuwa zai afka.
FETUR: Maimakon a samu saukin farashin man fetur bayan Buhari ya hau, sai ma kusan rubanyawa aka yi. Ayyukan da aka ce za a yi da kudin Karin fetur din kuma, jama’a na cewa ba su gani ba, domin duk bashi gwamnati ke ciwowa.
ASIBITOCI
Tunanin talaka da ya hau, to ya samu saukin kula da lafiya da kuma kudaden magani. Har yau bayan shekara hudu da hawan milki, ko sirinji ba a samu kyauta a asibiti.
An wayi gari a soshiyal midiya kullum ana neman taimakon yi wa yara da manya ayyukan tiyata a asibiti. Idan ba a hada kudin ba kuwa, babu wani asibitin gwamnati da zai yi wa mai ciwo tiyata. Sai dai ya fadi ya mutu. Ko da kuwa a wurin bin layin jefa kuri’a ya dauko ciwon.
TATTALIN ARZIKI
Duk wani shiri ko tsari wanda ba za a raya karkara ba, ba zai yi tasiri ga talaka ba. Yunwa da Buhari ya ce zai kora, ana ta zare mata idanu, amma ta ki fita daga cikin gidaje, ballantana ta tsorata ta fice ta bar gari.
KARIN ALBASHI
An shafe tsawon lokaci ana inda-inda da walankeluwa a wuri daya. A karshe gwamnatin tarayya ta ce ba ta iya biya wa ma’aikata bukata, har sai ta rage albashi. Ta ce na bukatar naira bilyan 580 duk shekara domin biyan karin albashi.
HARAJIN JIKI-MAGAYI
Watanni biyu kenan a jere kusan gwamnatin Buhari babu wani muhimmin abu da ta fi sakawa a gaba, kamar karin haraji kara bijiro da haraji.
An kawo batun kara harajin VAT daga 5℅ zuwa 7.5℅. An kakaba harajin ajiya da cirar kudade a banki. An fara tattara bayanai ma mutane milyan 45 da za a fara tatsar haraji a cikin su nan da karshen Disamba. Ana kokarin kakaba wa kangayen gidaje haraji. Ga kuma tunanin da wasu suka kawo shawarar a kakaba haraji a kan duk mai amfani da wayar GSM.
‘TOLLGATES’
Jama’a da dama sun cika da mamakin jin yadda gwamnatin ta tarayya ta ce aiki ya yi nisa wajen dawo da karbar kudade a ahingayen kan titinan gwamnatin tarayya a fadin Najeriya daga hannun direbobi.
RUSHE GINE-GINEN ‘YAN TIREDA
Ana bi ana rushe ‘yan shaguna da rumfunan masu karamin karfi a Arewa. Matasa da dama ma tafiya Kudu ko Abuja yin kananan sana’o’i inda nan din ma rusau ake yi a Abuja a kan ‘yan rumfunan masu kananan sana’o’i.
RUFE KAN IYAKA
Yayin da talaka ke kukan cewa an ki bada tsaro sosai ga al’umma, amma gwamnati ta fi maida fifiko wajen tsaron bushin shinkafa.
Jami’an kwastan na bi a daji ko tare hanya ko su shiga gari su na bindige mutane a kan buhun shinkafa.
Shin yaushe za a kai ga sauki a Nes Lebul?