Sakamakon binciken da kungiyar ‘Alive & Thrive Initiative’ ta gudanar ya nuna cewa mata da dama musamman wadanda suke aiki basu iya shayar da ‘ya’yan su nono na tsawon watanni shida saboda karancin kwanakin hutu.
Kamata ya yi mace ta samu hutun akalla watanni uku zuwa shida bayan ta haihu domin ta samu damar kula da kanta da dan da ta haifa. Sai dai hakan ba shine ke faruwa ba a kasar nan duk da cewa akwai dokar da ya ba mata hutun watanni shida sannan maza kuma watanni hudu.
Jami’ar kungiyar Abimbola Oduola ta bayyana cewa sun gudanar da wannan bincike ne a makarantu masu zaman kansu, masana’antu da asibitoci a fadin kasar nan.
Oduola ta ce sun gudanar da wannan bincike ne domin gano matsalolin dake hana kasar ta samu nasaran inganta kiwon lafiyar yara kanana duk da kokarin da gwamnati ke yi.
Ta ce mata da dama da suke aiki kuma suke shayarwa sun tabbatar cewa suna sane da mahimmancin shayar da ‘ya’yan su nono na tsawon watanni shida amma rashin samun isasshen hutu da rashin dakunan raino a wuraren aikinsu ke hana su.
“Mata da yawa sun ce hakura da aikin suke yi idan tura ya kai bango musamman idan babu mai raino ko mai taimaka musu.
Oduola ta bayyana cewa wuraren aiki da dama sun koka da yawan hutun da gwamnati ta ce a rika baiwa duk macen da ta haihu.
Sun ce idan suka fara yin haka aikin da ya kamata a yi a wuraren aikin ba zai yuwu ba kenan.
Oduola ta yi kira ga gwamnati da ta canja wannan doka ganin cewa wuraren aiki da dama a kasar nan basu iya bada wadannan yawan kwanaki.
Ta kuma ce gwamnati ta tilasta wa wuraren aiki bude wa mata wuraren rainon ‘ya’yan su.
Yin haka zai taimaka wa mata wajen kula da ‘ya’yan su yayin da suke aiki koda wuraren aikin su basu hutu ba.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya Ma’aikatar kiwon lafiya ta bayyana cewa kasa da kashi 24 bisa 100 na jarirai ne suke samun shayarwar uwayen su wato nono na tsawon watanni shida a kasa Najeriya.
Jami’in ma’aikatar kiwon lafiya Chimay Thompson ya fadi haka, sannan ya kara da cewa rashin yin haka na daya daga cikin dalilin dake kara mace-macen yara da mata.
Sai dai bincike ya nuna cewa haka na faruwa ne domin miliyoyin mata basa juriyar shayar da ‘ya’yansu nono na wannan tsawon lokaci.
Ya ce bincike ya nuna cewa shayar da ‘ya’ya nono zalla na tsawon lokaci na taimakawa wajen bada tazarar iyali, rage kiba, kare mace da kamuwa da hawan jini, kara dankon zumunci tsakanin uwa da ‘da.
Discussion about this post