RANAR ‘YANCI: Buhari ya maida Hukumomin Inganta Rayuwar Al’umma a sabuwar ma’aikata

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana sanarwar cewa an kirikiro sabuwar Ma’ikatar Ayyukan Jinkai da Inganta Rayuwar Jama’a domin ta rika gudanar da dukkan ayyukan raya al’umma da kuma tafiyar da shirye-shiryen ayyukan tallafa wa marasa da karfi da gwamnatin sa ta sa a gaba.

Ya yi wannan jawabi ne a cikin jawabin sa na Ranar Tunawa da Samun ‘Yanci, a safiyar yau Talata.

Daga cikin tsare-tsaren da Buhari ya maida a karkashin sabuwar ma’aikatar, mai suna Ministry of Humanitarian, Disaster Management and Social Development, har da shirin inganta marasa galihu na SIP, wanda ya ce shiri ne na naira bilyan 500 domin inganta rayuwar talakawa.

SIP ya kunshi shirin ciyar da ‘yan makaranta, shirin gwamnati na habbaka tattalin arzikin masu karamin karfi, shirin N-Power, bada basussuka ga kananan ‘yan tireda da masu sana’o’in hannu da kuma bayar da fallafi kai-tsaye ga iyalai marasa galihu da ake yi ta asusun ajiyar su na banki.

Kafin nan dai wadansu daga cikin wadannan aikace-aikace duk a karkashin hukumomi suke, wasu kuma a ofishin Mataimakin Shugaban Kasa ke kulawa da su.

Sadiya Garba ce Ministar wannan sabuwar ma’aikata. Dama kuma ma’aikatar ba ta fara aiki ka’in da na’in ba, saboda rashin takamaimen ayyukan da aka dora mata domin gudanarwa.

Sannan kuma Buhari ya yi magana a can ci gaban da aka samu a karkashin shugabancin sa a fannoni daban-daban.

Share.

game da Author