Mayakan Boko Haram sun cimma ajalinsu ranar Lahadi bayan afkawa bam din da suka dana wa sojojin Najeriya a Titin Lamba, dame jihar Barno.
‘Yan Boko Haram bakwai ne suka sheka lahira nan take inda wasu takwas suka kareraye bayan motan su ya yi kuskuren taka bam din da suka dan domin mamayan sojojin Najeriya.
Kakakin Bataliyan Soji dake jihar Barno, Kanal Aminu Iliyasu ne ya bayyana haka inda ya kara da cewa abin ya auku ne a daidai Boko Haram suna kan titin da ya hada Lamba-Jakana-Tarok.
Bayan haka Kanal Iliyasu ya kara da cewa dakarun Soji sun kama wani kasurgumin dan Sumugal da ya ke safarar kifi daga Chadi zuwa Najeriya tare da buhunan kifi makil a mota.
An gano cewa wannan kifi dashi ne idan aka siyar sai a rika siya wa ‘yan Boko Haram Magani, Abinci, Mai da dai sauran abinda suke bukata.
Baya ga haka kuma, a bankado wasu masu safarar irin wannan kifi daga Chadi a garin Mongonu, wadda suma sumugal suke yi ba tare da hukumomi sun sani ba.
” A irin wannan aiki da muke yi ne muka kama wani mai suna Musa Ishaku dauke da katin ID Card’ na rundunar Kwastam. Yana amfani da katin wajen zille wa sojoji dake aiki a iyakokin Baga.
” A Kaduna Kuma sojoji sun ceto dalibai 4 da aka yi garkuwa da su. Dakarun mu sun yi musayan wuta da maharan kafin Allah ya basu nasara akan maharan.
Discussion about this post