Hukumar Tsaron Sojojin Najeriya na neman wasu sojoji 22 da suka arce daga filin gumurzun yaki da Boko Haram.
Sanarwar kamar yadda wata majiyar manyan jami’an soja ta sanar da PREMIUM TIMES, ta ce idan aka kama su za su fuskanci kwakkwaran hukunci, saboda gudu da suka yi ana cikin fafata yaki da Boko Haram.
Sun arce ne a lokacin da gungun Boko Haram suka kai hari a wani sansanin soja da ke kusa da garin Gubio, a ranar 29 Ga Satumba. Wani yankin na Gubio har yanzu a hannun Boko Haram ya ke.
Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES an kashe sojoji 18 a wannan hari da aka kai ranar Lahadi da ta gabata, 29 Ga Satumba. Sai dai kuma wannan jarida ba ta tabbatar da adadin wadanda aka kashe din ba.
Amma kuma manyan jami’an soja da suka gaggauta tantance barnar da aka yi, a karshe sun gano cewa babu sojoji 22 sun gudu. Kuma a karkashin wani Manjo su ke.
An kai wannan hari ne wajen karfe 4:30 na yamma a ranar 29 Ga Satumba. Kuma tun a ranar aka nemi sojojin 22 aka rasa.
Yayin da babu gawar su, kuma aka hakikance ba kama su Boko Haram suka yi ba, an tabbatar da cewa tserewa suka yi.
Tun cikin watan Juli, 2018 Shugaban Sojojin Najeriya, Tukur Buratai ke nanata cewa duk sojan da ya gudu daga fagen fama zai fuskanci tsatstsauran hukunci.
Gudun da wasu sojoji ke yi daga filin daga na daya daga cikin manyan kalubalen da yaki da Boko Haram ke fuskanta a kasar nan.
Cikin Satumba, 2014, wajen sojoji 400 sun tsere cikin kasar Kamaru, a lokacin da Boko Haram suka kawo wata wawar-kora cikin Najeriya.
PREMIUM TIMES ta yi kokarin jin ta bakin Sagir Musa, Kakakin Yada Labarai na sojojin Najeriya, amma bai ce komai dangane da sojojin da ake nema ba.
SUNAYEN SOJOJI 22 DA AKE NEMA A HUKUNTA SU
Manjo U.A. Nagogo, Sajen Mallam Turaki, Sajen Benjamin Afolabi, Sajen Christian Nwachukwu, Sajen Patrick Kosin, Sajen Awuwa Orin, Sajen Ibrahim Amodu,Sajen Nasiru Umar, Sajen Bello Suleiman,Sajen Josiah Seth, Sajen Muazu Nura.
Kofur Ayodeji Ogunsuji, Kofur Michael Friday, Kofur Wakili Saul, Kofur Akyen Zamani, Kofur Yahaya Abubakar-Doia, Kofur Isikuru Venture, Kofur Aminu Isiaku, Kofur Usman Suleiman, Kofur Maigari Markus, Kofur Edward Ofem, Kofur Adams Shehu.
Discussion about this post