A wani rahoton musamman da PREMIUM TIMES ta yi in da ta zazzagaya wasu kauyuka dake kusa da babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, ta iske mafi yawan mata a gidajen su na girke ne da itace.
Likitoci sun tabbatar da hadarin da girki da itace ya ke yi wa lafiyar mutum a dalilin shakar hayakin iatace n da mata kan yi a lokacin da ake girki.
Wadanda Wakiliyar PREMIUM TIMES, Azeezat Adedigba ta garzaya har gidajensu a kauyukan Gazakia, Gwarko, Paikon Kore, Zhipe da Cheta duk sun bayyana mata cewa bakin talauci da wahala ne ya sa dole sai sun rika girki da itace domin basu da halin Kalanzir ko kuma Gas.
Dukkan su matan da aka tattauna dasu sun koka matuka cewa yin haka yakan sa su kamu da cututtuka da ya hada da Ulsa, ciwon Zuciya da dai sauransu.
” Ina so in tabbatar muku cewa wasu matan ma akan rasa su ne kwata-kwata a dalilin rashin lafiya da su kan yi fama da shi a dalilin shakar hayakin girki. Abin ya wuce kwatance fa.” In ji wata mazauniyar Gazaki.
Ita Aisha Zakare, cewa tayi a gidan haya take zama kuma dukkan su a gidan a wani dan daki suke girki. ” Idan muka iza girkin abinci hayaki ne ke turnike wa a cikin dan dakin nan sannan babu abinda za mu iya yi akai. Hakan kan sa kaga muna ta fama da cutar zuciya, tari da mura duk a dalilin wannan hayaki da muka shaka.
Illar shakar hayakin girki da itace
Wata likita mai suna Patricia Mmodu ta bayyana cewa hayakin da ake shaka a lokacin da ake girki da itace kan haddasa cutar Huhu da kuma ido baya ga yara suma da akan shiga da su a goye. Suma sukan fada cikin wannan matsaloli na rashin lafiya a dalilin wannan hayaki.
Sakamakon Bincike
Sakamakon binciken da majalisar dinkin duniya tayi (UN) ya nuna cewa akalla mutane 93,000 na mutuwa a dalilin shakar hayaki irin wannan a duk shekara Sannan kuma nan da shekaru biyar masu zuwa Najeriya za ta iya rasa mata 450,000 idan ba a gaggauta daukan mataki ba wajen kawar da wannan matsala na girke-girke da itace ba.