Asusun USAID, PEPFAR, Hukumar hana yaduwar cututtuka na kasar Amurka (CDC), Rundunar sojin Najeriya sun yi kira ga gwamnonin Najeriya da su maida hankali wajen dakile yaduwar cutar Kanjamau a kasar nan.
kungiyoyin sun fadi haka ne a wani ziyara da suka kai a sakatariyar kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ranar Talata a Abuja.
Jagoran kungiyar kuma darektan USAID Steve Haykin ya bayyana cewa Najeriya za ta yi nasara a dakile yaduwar kanjamau ne idan gwamnonin jihohin kasar nan suka hada hannu da gwamnatin tarayya wajen yaki da cutar.
“Samar da isassun magunguna da kayan gwaji na daga cikin gudunmawar da gwamnonin Najeriya za su iya bada wa a kasar nan.
Ya ce yin haka zai taimaka wajen kara yawan mutanen dake dauke da cutar kuma suke shan magani.
Idan ba a manta ba a shekaran 2004 ne PEPFAR ta fara tallafa wa Najeriya wajen dakile yaduwar kanjamau. Zuwa yanzu PEPFAR ta kashe dala biliyan 5.1 wajen yin haka.
Kafin wannan lokaci adadin yawan mutanen da ke dauke da cutar da gwamnatin Najeriya ke iya kula da su 5,000 ne kawai amma baya samun tallafin PEPFAR Najeriya ta samu nasaran bai wa miliyan 7.7 maganin cutar inda a ciki akwai mata masu ciki miliyan 1.6 sannan da yara marayu miliyan 1.1
Haykin yace akwai sauran aiki da dama da ya kamata a yi a kasan ganin cewa binciken da NACA ta gudanar a 2019 ya nuna cewa cutar ta yi wa yankin arewa maso gabashin kasar nan katutu.
A kashe Darekta -Janar din kungiyar gwamnonin Najeriya NGF Asishana Okauru ya bayyana cewa lallai zai aika da sakon kungiyar wa taron gwamnonin Najeriya.