A cikin nau’o’in aikin gona, noman shinkafa na a sahun gaba a ayyukan gonar da ake matukar shan wahala kafin amfanin gona ya kai lokacin da za a saka shi a tukunya, har a dafa a ci.
Tun daga shuka ko dashen irin shinkafa, har zuwa noman ta da girbin ta, duk aikin wahala ne. Wata sabuwar wahalar kuma ita ce daga ranar da aka fara girbe ta, ana shanyawa ta bushe, har zuwa sussukar ta da shikar ta da regewa har zuwa tsintar baragurbi da tsintar kananan tsakuwa, duk wasu wahalhalun ne sosai.
Sai kuma wahalar dauko ta ko jigilar ta daga gona a kai wurin sulalen ta, zuwa shanyar ta ta bushe da kuma dura ta a cikin buhu. A nan ma duk wahala ce matuka. Sai dai kuma wannan wahalar ba manya ko matasa kadai ta ta shafa ba, har da kananan yara ya gano a wani rangadin da ya yi a Jihar Taraba, inda ya ga yadda a wannan zamanin ba a amfani da injinan zamani a cashe shinkafa.
Wakilin mu da ya yi tattaki har a Karamar Hukumar Wukari ta Jihar Taraba, yadda masana’antun cashar shinkafa sama da 50 ke shan wahalar gaganiyar aikin shinkafa. Inda ya fara jefa kafar sa, shi ne wata masana’anta mai suna Injin Hajiya.
Hukumar Kula da Aikin Gona ta Amurka, ta bayyana cewa Najeriya na noma shinkafa tan milyan 3.7 a kowace shekara. Da yawan wannan tulin shinkafa kuwa daga jihar Taraba ake noma ta.
Jihar Taraba na daga cikin jihohi 10 da aka fi noma shinkafa da damina da kuma noman rani a Najeriya. Haka dai rahoton GEMS4 ta tabbatar.
Garuruwan da ake aikin noman shinkafa a Taraba a lokutan rani da damina, sun hada da Wukari, Tsukundi, Rafin Kada, Donga Suntai da sauran wasu kauyuka da dama.
Nau’o’in shinkafar da su ke nomawa, sun hada da Sipi, Faro, Yarhai, Abari da kuma Parogidi.
Duk wannan tulin shinkafar da suke nomawa, idan sun kwashe ta, su na nufa da ita ne a masana’antun gyaran shinkafa a garin Wukari, wadanda ke hanyar fita zuwa garin Takum da kuma kan titin Jalingo Road.
Sai dai duk da kururuta makudan kudaden da gwmnatin tarayya ke kashewa wajen inganta noman shinkafa, a wajen aikin rege da da cashe ta da shikar ta da sulala ta duk babu wata hanyar amfani da na’urorin zamani. Duk ci-da-karfi ake yin ayyukan.
A wasu masana’antun casar shinkafar a Wukari, kafin a gyara shinkafa a kan dauki akalla kwanaki biyar, wasu lokutan ma har makonni, saboda matakai daban-daban da ake dauka. Sannan kuma babu sauri, saboda rashin kayan aiki na zamani irin yadda wasu kasashe kamar Chana ke amfani da su.
Duk wadannan aikace-aikace karti ne ke yin su, sai kuma mata da tulin kananan yara.
MATSALAR JIGILAR SHINKAFA DAGA KAUYUKA ZUWA WUKARI
Mathias Rahila attajirar kauye ce. A da can kauyuka ta kan shiga ta rika sarin shinkafa daga manoman kauye ta na cashewa a garin Wukari ta sayar ta samu riba.
Amma a yanzu saboda yawaitar rikice-rikice da kashe-kashen kabilanci da ya addabi Jihar Taraba, Rahila ta daina shiga kauyuka sarin shinkafa.
“A da kauyuka mu ke shiga mu na sayo shinkafa. Amma sai mu ka daina, saboda rikice-rikicen da ake yawan yi. A yanzu kuwa a nan garin Wukari suke kawowa mu saya.” Haka ta shaida wa PREMIUM TIMES.
“Mu ka dan fita kauyukan da ke kusa da gari mu sayi shinkafar, amma hakan ma mu kan samu matsala da ‘yan sanda, wadanda ke kafa shingaye a kan titi, su na karbar naira 50 daga kowanen mu.
Wadannan kudade da mu ke bayarwa a duk inda mu ka samu ‘yan sanda, su ke rage mana ribar da mu ke samu. Wani lokaci sai ka ga kusan su mu ke yi wa wahala kawai.”
YADDA YARA KANANA KE AIKIN GYARAN SHINKAFA
Akalla sauran matakan gyaran shinkafa uku, duk yara kanana ne ke yin aikin. Su ke wanke shinkafar, su ke dafa ta ko sulala ta a cikin manyan diro-diro, kuma su ke aikin shanyar ta domin ta bushe.
Sannan kuma su ke karakainar kwashewa daga wurin shanya su na kaiwa inji, inda ake durawa a buhuna.
Cikin kananan yaran da ke wannan aikin wahala ko aikin karfi, har da Joshua Simon da dan uwan sa, Caleb, wadanda tagwaye ne masu shekaru 14. A duk lokacin hutu, sai su baro garin Jalingo su je Wukari domin aikin shinkafa a wurin kawun su. Aikin su shi ne wanke shinkafa da kuma rege tsakuwa da kwafsa.
Aikin na su aikin wahala ne. Da farko sai sun yi amfani da ‘wheel barrow’ sun dauki shinkafar daga dakin ajiya a kan amalanke, sannan su je wurin wankewa, su sheka ta cikin diro wanda ke cike da ruwa.
Bayan sun gama wankewa kuma sai su kai ta rana ta bushe, sannan kuma su sake kwashewa su zuba a buhuna su maida dakin ajiyar shinkafa a killace ta.
Bayan sun kammala wannan wahalhali, ladar su ita ce naira 500 a kowane buhu 14 da suka wanke.
“Bayan mun gama aikin, idan mun koma gida mu kwanta, mu kan kasa yin barci saboda tsananin kaikayin da jikin mu ke yi. Amma wannan bai damun mu, a haka za mu sake komawa da safe mu ci gaba da aikin.” Cewar Caleb.
A gefen su akwai wani dattajo mai suna Umar, wanda ya kai shekaru 60 da haihuwa, shi kuma aikin sa shi ne sulala shinkafar.Katon murhu ne Umar ya hada, wanda ya ke bankawa wutar itace, ya na zuba shinkafar cikin wani katon bangaji na alminiyan ya na sulala shinkafar a ciki. A duk buhu daga mai nauyin 50kga, Umar ya na cajin naira 200.
Idan aka zuba shinkafar cikin ruwa, mu kan bar ta sai ta kwana daya cur a cikin ruwan zafi. Sannan a rana ta biyu, sai mu kwashe ta mu sake zuba ta cikin wani ruwan. To duk wata kwafsa za ta wo sama, sai a rika kwashewa ana zubarwa. Daga nan sai a baza ta kasa ta bushe.
Umar ya ce zafin wuta na damun sa, sau da yawa idan ya tashi daga aiki, ba ya iya barci, har sai ya sha madara tukunna.
Yara masu tura kura, ko kuma ‘wheel borrow’, su ma wata bakar wahala su ke sha wajen dako da jigilar shinkafar. Ana biyan su naira 600 ko 700 tun safe har dare idan suka yini aiki.
MUMMUNAN CAMFI A AIKIN SHINKAFA ‘YAR HAUSA’
Saad Bala na daya daga cikin matasa da dama masu aiki da Injin Hajiya. Shi ma aikin wahala ne, kuma tattare ya ke da camfe-camfe.
“An ce idan mutum ya kwana da mace, to washegari kada ma ya tayar da injin din.
Sai dai a ba wani ya tayar. Domin idan ka tayar, to ba zai tashi ba. Idan kuwa ya tashi to zai ji maka ciwo. Kamar yadda ya taba ji min ciwo nan a kafa ta da ka ke gani.
“Shi wannan inji tamkar mutum ya ke. Idan ka kwanta da mace, ko ka tashe shi ba zai tashi ba. Idan ka zo wurin aiki ba ka yi wanka da safe ba, ko ka tada inji ba zai tashi ba. Wannan al’ada ce rikakkiya.
“Misali, yanzu idan injin na ba ka matsala, za a tambaye ka, shin ka je ka kwanta da mace jiya? Ka kuwa yi wanka da safe kafin ka fito?
Shi ma aiki da injin din akwai camfi a cikin sa. Idan mutum ba mai gaskiya ba ne, ko kuma ya aikata rashin gaskiya a lokacin da ya ke aiki da injin din na aikin shinkafa, to zai ji masa ciwo, kamar yadda Saad ya yi ikirari.
Farkon lokacin da wakilinmu ya fara isa ‘Enjine Hajiya’, ya samu Saad ya na ta kiciniyar tayar da inji, amma ya ki tashi. Kwanaki biyu aikin bai yiwu ba.
Shin ko Saad shi ma kwanciya da wata mata ya yi har Injin Hajiya yak i tashi? Ko kuwa wankan safe ne bai yi ba? Wakilinmu dai bai tambaye shi dalili ba. Shi ma bai shaida wa wakilinmu dalilin ba.