Gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya ce surutan da wasu dibgaggu ke yi cewa wai shi matsafi ne, abin dariya ne kawai.
Ortom ya yi wannan bayani a wani taron kwanaki biyu na sanin-makamar-aiki ga sabbin nade-naden ma’aikatan da gwamnan ya yi a Makurdi, babban birnin jihar.
Gwamnan ya ce shi ya yi wankan Baftisimar zama cikakken Kirista mai tawali’u ga ubangiji tun cikin 1979.
Daga nan ya kara da cewa tuni shi ya mika wuya ga Yesu Almasihu a matsayin mai ceton sa. Don haka babu ruwan sa da tsafi ko matsafa, bai taba yi ba, kuma ba zai taba yi ba.
Daga nan sai ya ce ya sani sarai ana watsa ji-ta-ji-ta kuma masu adawa na yi masa yarfe da sharri wai shi matsafi ne. Sai dai kuma ya ce abin ba ya damun sa, sai ma dariya kawai ya ke ba shi.
“Ba zan manta ba, akwai ma lokacin da wasu mutane suka nemi su tsaida ni daga jawo aya a cikin Bebul, a lokacin da na ke wani jawabi.”
Ortom ya ce wannan ya ba shi mamaki matuka.
“Na ji wasu mutane na cewa wai Ortom shi ne shugaban matsafan Jihar Benuwai. To ba gaskiya ba ne. Ni dai na kasance mai tsoron ubangiji na. Shi na rike ba tsafi ba.
“Wata rana a wurin bukin bizne wata gawa, mutane suka zarge ni wai ina kokarin na jawo ayoyi daga cikin Bebul na yi tsafi da su. Suka ce wai kada a bar ni na jawo aya ko daya. Wai idan aka bari na jawo aya daga Bebul, to duk jama’ar da ke wurin ba za su iya bude baki su yi magana ba.” Inji Ortom.
Ya kara da cewa babu wani dan Adam da ya taimaka masa ya zama gwamna, shi abin sa ikon Ubangiji ne kawai.
“Ni tun cikin 1992 Ubangiji ya yi min ishara cewa wata rana zan zama gwamna. Sai cikin 2015 ubangiji ya ida nufin sa.”
Ya ce ya fuskanci kalubale sosai, domin a cikin 2017 ma har ya yanke shawarar cewa idan 2019 ta zo, ba zai sake tsayawa takara zango na biyu ba.
“Amma da ya ke Ubangiji na dogara da shi, sai ga shi ma masu adawa da ni a baya, su ne suka taya ni kamfen.” Inji Ortom.
Ortom ya ce da ubangiji ya dogara, don haka ba shi da wani ubangida a siyasa.