Kungiyar rajin sa-ido a kan yadda ake kashe kudaden ayyukan gwamnati, wato NEITI, ta yi kara ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta gudanar da binciken yadda Hukumar Inganta Manyan Makarantu (TETFUND) ta kashe naira bilyan 999.3 a cikin shekarun 2012 har zuwa 2016.
NEITI ta ce wannan kira da ta yi ya zama wajibi sakamakon wani bincike da ta yi, inda ta ce ta gano TETFUND ba ta da wani takamaimai ko tartibin jadawalin kididdigar yadda ake kashe kudaden gudanar da ayyuka.
Sai dai kuma ita TETDUND ta karyata dukkan zarge-zargen da NEITI ta yi ma ta, kamar yadda za ku karanta nan gaba.
NEITI ta ce Asusun Gwamnatin Tarayya ya bai wa TETFUND naira bilyan 804.9 daga 2012 zuwa 2015 daga harajin da aka karba daga kamfanonin albarkatun kasa.
Sannan kuma an bai wa TETFUND naira bilyan 188.3 daga harajin kamfanonin da ba na albarkatun kasa ba.
Damuwar da NEITI ta nuna ita ce duk wani kokari da ta yi domin hukumar TETFUND ta ba ta kwafe-kwafen jadawalin kudaden da ake kashewa ko na aikin da aka yi, ya ci tura.
Komai namu a fili yake, Inji TETFUND
PREMIUM TIMES ya nemi jin ta bakin Kakakin Yada Labarai na TETFUND, Arolesafe, wanda ya karyata zarge-zargen da NEITI ta yi.
Ya ce, “a duk shekara TETFUND ta na buga kundin ayyukan ta, wanda ke kunshe da kudaden da suka shigo, yadda ake kashe su da kuma ayyukan da aka yi da su. Hatta kundin 2018 ma ya fito, an buga shi tuni.”
Inji Arolesafe wanda ya ce NEITI za su iya bincikar na 2012 har ma zuwa 2016 da na 2018.
Sannan kuma ya karyata furucin da NEITI ta yi cewa daga Asusun Gwamnatin Tarayya ake bai wa TETFUND kudi. Ya ce kudin TETFUND daga Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida (FIRS) ya ke fitowa, ita karba ko karbo ma ta kudaden ta.
Discussion about this post