A wani abu mai kama da an ki cin biri an ci dila, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta kashe makudan kudade har naira bilyan 450 wajen biyan kudaden tattafin man fetur a cikin shekarar 2020 mai shigowa.
Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, duk kuwa da kokarin da gwamnatin ke yi cewa za ta gyara dukkan matatun man kasar nan, domin a daina shigo da tattacen man fetur daga kasashen waje.
Idan ba a manta ba, tsohon ministan man fetur, Ibe Kachikwu ya bayyana cewa NNPC zai daina shigo da tataccen man fetur daga waje zuwa cikin kasar nan a cikin 2019. Amma dai duk da cewa ba a sake nada shi minista ba, har yau ba a daina shigo da man ba, kuma babu ranar dainawa, domin 2019 ta kusa kaiwa karshe.
Ministar Kudi ta yi wannan karin hasken makudan kudaden da za a kashe a 2020 har naira bilyan 450 wajen biyar kudaden tattafin mai, wato ‘subsidy’, a wurin wani taron karin haske kan kasafin kudin 2020 da aka gudanar a Abuja.
Zainab ta yi wannan bayani ne a lokacin da Shugaban Kungiyar Masu Masana’antu na Kasa (MAN) Mansur Ahmed, ya tambaye ta shin ko an cire biyan kudin tallafin mai, ko kuwa har yanzu ana biya?
Kudaden dai a karkashin mulkin Buhari, ana yi musu alaye da kiran su kudaden cike gurbi, domin a karkashin wannan gwamnati ta sa, NNPC ce da kan ta kadai ke shigo da mai daga waje.
Idan ba a manta ba kuma, cikin watan da ya gabata ne sabon Shugaban NNPC, Mele Kyari, ya bayyana cewa za a gyara dukkan matatun mai hudu na kasar nan da ke Fatakwal, Warri da Kaduna.
Kyari ya tabbatar da cewa nan da 2022 za a gyara dukkan matatun mai hudu da ke kasar nan.
Ba dai wannan ne karon farko da aka rika daukar alkawarin gyara matatun main a kasar nan ba.
Na baya-bayan nan shi ne na tsohon Minista Kachikwu, wanda ya ce kafin karshen 2019 za a gyara dukkan matatun mai na kasar nan.
A lokacin da jam’iyyar APC ke jam’iyyar adawa, zargi gwamnatin Jonathan da biyan kudaden tallafin mai, tare da cewa damfara ce.
Bayan APC ta hau mulki, ta kasa cika alkawarin rage kudin mai daga lita daya kan naira 86, sai ma karin kudin lita ta yi zuwa naira 155, tare kuma da ci gaba da biyan kudin tallafin mai.