Najeriya ta sanar da dakatar da aiyyukan Wasu kungiyoyin bada agaji biyu sake aikin jinkai a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke jihar Barno.
Gwamnati ta yanke wannan hukunci ne domin inganta aiyukkan jami’an tsaro a jihar ganin cewa Ana zargin wadannan kungiyoyi da yi wa Najeriya zagon kasa a aikin kawo karshen Boko Haram.
Ministan aiyukkan jinkai Safiya Umar ta sanar da haka a zantawa da manema labarai da ta yi a Abuja ranar Alhamis.
Ta ce yin haka zai taimaka wa gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyin mutanen da hare-haren Boko Haram ya illata a jihar.
Wannan sanarwa ya fito ne makonni biyu bayan rundunar sojin Najeriya ta tsaida aiyukkan agaji na wasu kungiyoyin bada tallafi na kasashen waje sake aiki a jihar.
Wadannan kungiyoyi kuwa sun hada da ‘Action Against Hunger da Mercy Corps’.
Rundunar sojin Najeriya ta yi haka ne bayan zargin wadannan kungiyoyi da samarwa Boko Haram da abinci, magunguna da fetur da suke yi.
A dalilin haka gwamnati ta ce za ta yi aiki da kungiyar bada tallafi ne a jihar idan aiyukkan kungiyar ya Yi daidai da tallafin da ‘yan gudun hijira ke bukata sannan kuma aiyukkan ba zai kawo wa dakarun cikas a aikin su ba.
A karshe jakadan tarayyar kasashen Turai (EU) a Najeriya Ketil Karlsen ya bayyana cewa EU a shirye take domin tallafa wa mutanen jihar Baro.
Karlsen yace domin ganin hakan ya faru EU ta bada Najeriya tallafin Euro miliyan 200.
Discussion about this post