Mutane milyan 94.5 ke cikin fatara da talauci a Najeriya -Oxfam

0

Cibiyar Bin Diddigin Yunwa, Fatara Da Talauci ta Duniya, wato Oxfam, ta bayyana cewa akwai mutane milyan 94, 470, 535 wadanda fakiranci da talauci ke neman kassarawa a Najeriya.

Daraktan cibiyar da ke Najeriya, Constant Tchona ne ya bayyana haka a Abuja, jiya Litinin.

Ya yi wannan bayani ne a wurin wani taron sanin makamar kamo bakin zaren maida hankali wajen tsamo milyoyin jama’a daga halin kaka-ni-ka-yi da su ke ciki.

Tchona ya ce wadannan mutane kusan milyan 100, daga cikin su babu mai iya samun akalla naira 684 a kullum, wadanda akalla su ne adadin da ake ganin duk talauci da fakirancin dan Adam a kasar nan, a ce ya na iya samun su a rana.

Oxfam ta nuna cewa akwai fa gagarimar matsala ta fakiranci, wanda ya ma fi talauci muni a Najeriya.

Cibiyar ta ce a cikin watan Afrilu da ya gabata, adadin fakirai a Najeriya su milyan 91, 501, 377. Amma ya zuwa watanni shida a yanzu, an samu karin har milyan 2, 969, 158 kenan.

Oxfam ta ce Najeriya na daf da zama kasar da ta fi kowace kasa a duniya yawan matalauta da masu fama da kuncin rayuwa.

“Nan da shekarar 2030, kashi 25 bisa 100 matalauta da fakirai na duniya za su kasance a Najeriya su ke.

“Kuma gwamnatin na sane da yawan masu fama da kuncin rayuwa a kasar nan sun kai adadin milyan 94 din nan. Domin Shugaba Muhammadu Buhari da kan sa ya ce nan da shekaru 10 gwamnatin sa za ta ceto mutane milyan 100 daga fatara da talauci.”

Oxfam ta ci gaba da yin nunin cewa yawan al’ummar Najeriya a yanzu haka sun kai milyan 200, 963, 599. Don haka zuwa shekarar 2050, Najeriya za ta kasance kasa ta uku a yawan al’umma a duniya.

Share.

game da Author