Mutane 13,700 cikin 41,000 ne suka yi nasara a matakin farko na neman aikin jihar Kaduna

0

A ci gaba da shirin daukan sabbin ma’aikata da gwamnatin jihar Kaduna ta ke yi, a ranar Laraba, gwamnatin ta bayyana sunayen mutane sama da 13,000 da suka tsallake matakin farko.

Gwamnatin ta ce mutane sama da 41,000 ne suka cika fom din neman aiki a jihar, sai dai kuma mutane 13,700 ne suka samu tsallakawa zuwa gwajin gaba.

A bayanan ga gwamnati ta fitar mutane 381 ne aka zabo da jihar Kogi, Kwara 181, Legas 176, Ogun 86, Imo 63, Anambra 60, Osun 74, Oyo 154, Kaduna 10, 696, Benuwai 266, da dai sauran jihohin kasar nan.

Gwamnati ta umarci duk wadanda suka nemi aikin da su duba shafunan neman aikin na jihar da kuma akwatunan sakon su na yanar gizo domin dubawa ko suna cikin wadanda suka yi nasara a wannan karo na farko.

Gwamnati ta tura ma wadanda suka yi nasara sako donmin shirin gwaji na gaba.

KDSG Recruitment State list Page 2

KDSG Recruitment State list Page 2

Share.

game da Author