Mutane 100,000 ke kamuwa da ciwon shanyewar barin jiki a Najeriya duk shekara – NSO

0

An bayyana cewa akalla mutane 100,000 ne ke kamuwa da ciwon shanyewar barin jiki a Najeriya.

Kungiyar Masu Kula da Fama da Ciwon Shanyewar Jiki ta Kasa ce, NSO ta bayyana haka a cikin wani bayanin bayan taro da ta fitar yau Talata a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Sanarwar wadda Shugaban Kungiyar, Abayomi Ogun ya bayar, ta kara da cewa a duk cikin mutane hudu, mutum daya kan kamu da ciwon shanyewar jiki a rayuwar sa.

Sannan kuma Abayomi ya kara da cewa tabbas wannan ciwo za a iya kauce wa kamuwa da shi matsawar aka kiyaye matakan kauce wa kamuwa da shi.

Daga cikin musabbabin kamuwa da ciwon, Abayomi ya ce har da ciwon hawan jini, yawan cin nama, kiba, ciwon suga, gajiya, ciwon bugun zuciya, yawan shan gishiri, taba sigari da sauran su.

Ya ce ya kamata a rika cin korayen ganyaye da kuma yawan motsa jiki.

A cikin 2015 dai bincike ya nuna cewa akwai akalla mutane milyan 14.5 masu fama da ciwon shanyewar jiki a Najeriya.

Sannan kuma akwai milyan 80 da ke fama da ciwon a duniya baki daya.

Share.

game da Author