Matsalar tsaro abu ne wanda ya addabe mu a Najeriya musamman a Arewacin Najeriya. Matsalar tsoron ya hada da masu garkuwa da mutane, barayin shanu, yan bindiga dadi da sauransu.
Ba shakka wannan matsalar tsaron ya jefa mutane cikin wani mummunan hali domin dayawan mutane sun daina zuwa gurin niman abinda zasu ci, musamman manoma da matafiya da sauransu.
A gefe daya, gwamnati tace tana iya kokarinta taga ta daidai ta komai yadda suka kamata. Amma a nawa guntun tunanin ba wai gwamnati zata yi kokarin magance wannan matsalar tsaron na wannan lokacin bane kawai.
Akwai abubuwan da gwamnati ya kamata su duba bayan yaki da wannan matsalar tsaron da suke yi saboda gaba kada a sake fada irin wannan halin idar har an samu an magance wanda ake fama dashi yanzun. Zaa ayi nasaran magance matsalar tsaron da muke fama dashi yanzun, amma idan baa magance abubuwan da suka haifar da matsalar tsaron ba a gaba zaa iya komawa idan jiya wanda muna addu’a Allah ya kiyaye. Allah kuma ya kawo mana saukin wanda muke fama dashi yanzun.
Ya kamata gwamnati ta tayi nazari akan wadanda Abubuwa;
Na daya, shin suwa ke aikata wannan miyagun ayyukan?
Na biyu, shin masu aikata wannan miyagun ayyukan sunyi karatun addini ko na kobo?
Na uku, shin mai saanarsu kafin su shiga wannan miyagun ayyuka?
Ba shakka idan har zaa duba wadannan abubuwa kuma ayi nazari a kansu, toh ta nan ne zaa samu saukin magance matsalar tsaron da muke fama dashi kuma a kiyaye sake fadawa cikinsa a gaba da iznin Allah.
Ba shakka mafi yawancin wadanda ake kamawa da aikata wadannan ayyukan matasa ne. Kuma mafi yawancinsu idan aka tambayesu akan ko sunyi karatu na addini ko boko, sai su ce duka babu wanda suka yi. Kaga kuwa mutumin da baida ilmi komai ma zai iya aikawa domin baya tunanin gamuwansa da Allah.
Kaga daga nan gwamnati sai ta fahimci rashin ilmi na daya daga cikin abinda ya kawo wannan matsalar tsaron da muke fama dashi. Sai gwamnati tarayya tare da gwamnatin jihohi arewacin Najeriya su fitar da tsari wanda zai bawa kowa daman kai yaronsa makaranta a kyauta daga Primary zuwa Secondary, sannan su kafa dokan duk wanda bai kai yaronsa makaranta ba zaa hukunta shi kamar yadda naga gwamnatin jihar Kaduna suka yi. Sannan jami’o’in mu (Universities) na arewa a rage kudin makaranta ta yadda talaka zai iya kai yaronsa, kuma gwamnati su dinga daukan nauyin wadansu daga cikin marasa karfi.
Ba shakka idan har gwamnati zata yi haka, toh da iznin Allah zaa samu saukin matsalar rashin ilmi da tsaron da muke fama dashi a arewacin Najeriya.
Haka a cikin wadannan yara masu aikata wannan miyagun ayyukan zaka samu akwai wadanda sunyi karatun amma ba aiki. Toh saboda gajertar hakuri sai su fada cikin miyagun aikin. Saboda haka dole gwamnati zasu kara kokari gurin samarwa matasa aikin yi, domin rashin aikin yi shima ya taimaka gurin matsalar tsaro sosai, wanda dole sai gwamnati ta fitar da tsari na musamman domin samarwa matasa aiki.
Ba yadda zaayi gwamnati ta baiwa kowa aiki, amma idan suka gyara masana’antun mu na arewa da aka rufe, suka sake karo wadansu, toh wallahi ba shakka kashi sittin zuwa saba’in (60-70%) na matasanmu zasu samu aikin yi. Ba shakka idan aka rage yawan matasa marasa aiki yi, shima zai taimaka gurin kawo mazan lafiya.
Idan har gwamnatin tarayya da gwamnonin arewa zasu dauki wadannan matakai da iznin Allah zamu magance matsalar tsoro, rashin aiki da rashin ilmi cikin sauki a arewa.
Amma idan suka ce ba haka ba, idan suka hau mulki daga su sai yaransu da abokansu babu ruwansu da talaka, zasu bar talaka da talauci, ba ilmi, ba inganceccen lafiya. Toh ba shakka idan ba Allah ya kiyaye ba zaa zo lokacin da, dasu da yaransu kasannan sai ya gagaresu zama sakamakon mulkin zalunci da suka yi.
Saboda haka ya kamata suyi amfani da daman da Allah ya basu su taimakawa al’ummarsu ne bawai su cutar dasu ba saboda son duniya.
Allah ya bamu zaman lafiya a Nigeriya. Allah ya bamu damina mai albarka, ya kuma ba shuwagabanninmu zuciyar tausayinmu, suyi mana shugabanci nagari.