Masu garkuwa da mutane sun sace mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ACP Musa Rambo a hanyar sa ta zuwa garin Jos a iyakar Kaduna da Nasarawa.
Kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo ya bayyana wa manema labarai cewa, an tsinci motar mataimakin kwamishina Rambo ne a kusa da Jos daidai dajin Kanock.
An ajiye motar a gefen titi, sannan aka ajiye Katin shaidar sa na ma’aikaci a cikin motar, wato ID card.
A wani rahoto da jaridar Punch ta wallafa, ta ce zuwa yanzu maharan sun kira ‘yan uwan kwamishina Rambo suna bukatar a biya naira miliyan 50 kudin fansa.
Sai dai kuma Sabo ya ce tuni har ‘yansanda sun fantsama danin Kanock domin farautar wadannan mahara da kuma ceto mataimakin kwamishina Rambo.
Sannan bai ce komai ba game ko maharan sun nemi abiya kudin fansa ko a’a.