Kodinatan dalibai masu bautan kasa NYSC na jihar Kano Ladan Baba ya bayyana cewa dalibai 26 ne za su maimaita aikin Yi was kasa hidima a jihar Kano.
Baba ya fadi haka ne da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Juma’a a wajen yaye masu bautan kasa da suka yi aiki a jihar Kano.
Ya ce a bana NYSC ta yaye dalibai 1,942. Ciki akwai maza 1,220 sannan mata 719.
Cikin wadanda suka yi nasu hidiman a Kano, 26 za su sake saboda kin zama a wuraren da aka tura su.
Saboda haka su zasu kammala ayyukansu cikin watanni hudu.