Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN), reshen Jihar Adamawa, ta yi kira ga babban bankin Najeriya, CBN da ya sassauta wa manoman wajen biyan kudaden rance da suka amsa domin noman shinkafa.
Kungiyar wadda shugabanta, Stephen Maduwa ya yi wannan roko ta bayyana cewa manoman sun yi asarar gaske a bias ambaliya da ya ci gonakin su.
Maduwa yace kafin wannan ambaliya manoman suna sa ran samun girbi mai yawan gaske sai dai kash, gaba daya yanzu hannun agogo ya koma musu baya a dalilin haka.
“ Ba karamin asara manoman mu suka yi ba wadda a dalilin haka muke ganin biyan bashin zai yi wa manoman matukar wuya yanzu.
Haka shima shugaban manoman shinkafa da masara reshen jihar Adamawa Phineas Elisha, ya koka kan wannan matsala da manoman yankin suka fada.
“ Mafi yawan manoman jihar duk sun kammala girbi suna shirye-shiryen kwaso amfanin gona ne zuwa gida sai wannan ambaliya ya zo. Sun rasa kusan komai ne a dalilin wannan ambaliya.
“ Shinkafa, Masara da duk wani abu da muka noma mun yi asarar su a dalilin wannan ambaliya. Ina rokon gwamnati ta kawo mana dauki game da wadannan basussuka da manoma suka ci kuma suka yi asarar kayan gona.
KARANTA: Ambaliya ta malale gonakin shinkafa da na masara a Adamawa
Idan ba a manta ba tun a watan Satimba ne Kungiyar Manoman Shinkafa na jihar Adamawa, ta bayyana cewa manoma sun rasa amfanin gona a dalilin tafiyar-ruwa da gonakin shinkafar manoma sama da 5000.
RIFAN ta ce wannan kuwa babbar barazana ce ga yalwar abincin da tun da farko ake ta murnar za a samu a kakar bana.
Shugaban Kungiyar ne na Jihar Adamawa, Mista Maduwa ya bayyana haka a lokacin da ya ke hira da manema labarai, ranar Litinin a Yola, jihar Adamawa.
Maduwa ya kara da cewa wadda ke da mabobi 7, 000 masu rajista a jihar, har yanzu ba ta kammala tantance iyakar munin barnar da ambaliyar ta yi wa manoma ba.