Sanata Rochas Okorocha ya ci kasuwar sa yau Alhamis a zauren Majalisar Dattawa, inda ya tashi ya yi kiran cewa a rage yawan sanatoci da mambobin Majalisar Tarayya, saboda ba su da wani amfani sai haifar da kara kashe kudade.
Ya ce kamata ya yi kowace jiha a ce sanata daya ne zai wakilce ta. Sannan kuma dan majalisar tarayya uku ne zai wakilci kowace jiha.
Okorocha, wanda shi ke wakiltar Shiyyar Imo ta Yamma, ya ce irin yanayin halin da ake ciki a kasar nan, to idan ana so abubuwa su fara yin daidai, sai an bi an rage duk wata hanya da ake kashe kudade barkatai.
Sanatan ya mike ne yayin jawabi a kan Tsari da Fasalin Kudaden da Gwamnatin Tarayya za ta Kashe daga 2020 zuwa 2022. Kwamitin duba tsarin ne wanda Buhari ya aika wa Majalisa suka gabatar da aikin dubawa a yau Alhamis.
Tsohon gwamnan na Jihar Imo, ya ci gaba da cewa:
“Wane aiki ne sanata uku zai iya yi wanda sanata daya ba zai iya yi ba?
Gunaguni
Yayin da Rochas ya zo daidai da bayanin sa, sai sanatoci suka rika yi masa gunaguni. Sai dai shi kuma bai fasa furta duk abin da ya yi niyyar bayyanawa ba.
” Mu yanzu a nan kowace jiha na da sanata uku. Can a Majalisar Tarayya kuma ga majiya karfi mutum 360 can a zaune reras. To rage wannan yawa zai kawo rage kashe kudade.
“A wannan zubin sanatoci zango na 9, babu wani abin da mu ka yi da ya bambata mu da na zango na 8 da na 7 da na 6 har ma da na 5. To idan babu wani banbanci, ai babu wani canji kenan. An ki gudu, ana tuma tsalle kawai wuri daya.” Inji Okorocha.
A karshe dai Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya bukaci Okorocha ya gabatar da batun sa a matsayin kudiri a Zauren Majalisa.
Okorocha dai abin da ya yi kira shi ne, gaba daya yawan ‘yan majalisa ya tashi daga 469 ya koma 146 kawai.