Ma’aikatan boge ne suka zame wa gwamnatin Bauchi kashin Kifi a wuya – Gwamna Bala

0

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya koka kan yadda ma’aikatan boge suke zame wa gwamnatin jihar Bauchi kashin kifi a wuya.

Gwamna Bala ya bayyana haka ne a yayin da yake rantsar da sabon shugaban ma’aikatan jihar, Abubakar Maaji da wasu sabbin shugabannin ma’aikatu.

Bala ya bayyana cewa babban abin da ya fi tada masa hankali shine yadda aka ciki jadawalin ma’aikatan jihar da sunayen boge sannan kuma da yadda wasu manyan ma’aikata suke karbar albashi har na mutane biyu zuwa sama ba tare da wadannan mutane da aiki ba kawai na boge.

” Wannan matsala shine ya fi tada min da hankali da dole a matsayinka na sabon shugaban ma’aikata ka bi diddigin wannan matsala kuma ka bankado mana irin wadannan mutane da sunayen da ba na ma’aikatan gaske bane.

Gwamna Bala ya kara da cewa akwai matasa da dama da suka kammala karatun su na jami’a da kwararru da dama a jihar amma da saboda cika ma’aikatun gwamnati da akayi da ma’aikatan karya aba aiya daukan su aiki ba.

Akarshe ya yi kira ga Maaji da ya tabbata ya yi aiki tukuru wajen ganin an kawo sauyi a aikace aikacen gwamnati da ci gaba.

Idan ba a manta a kwanakin baya ne gwamnan Bala ya dakatar da albashin wasu ma’aikata har 41,000 da aka gano basu da lambar mallakar asusun baki na dindindin. Hakan na nuni cewa dama can ba ma’aikatan gwamnatin jiha bane.

Gwamna Bala ya ce ce ba za a biya masu dannan sunaye ba har sai sun mika shaidar banki na BVN tukuna.

Jihar Bauchi da tana matsayi na 25 ne a jerin jihohin dake da tara mafi karancin kudaden shiga a kasar nan.

Rahoton hukumar Kididdiga ta Kasa NBS, ya nuna cewa baya jihar Bauchi na iya tara naira biliyan 9 ne da ‘yan kai a duk shekara wanda ke nuna baya wuce naira miliyan 800 ne kacal take iya tarawa a duk wata kudaden haraji da mutane ke biya.

Share.

game da Author