Lauya ya zargi ‘yan sanda da binne laifin fashi da makami

0

Wani lauya mai suna Benjamin Ogunmodede, ya rubuta wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda korafin cewa ‘yan sanda a jihar Ogun na kokarin danne laifin fashi da makamin da aka yi wa wanda ya ke karewa, mai suna Olalekan Olakitan.

Lauyan ya ce an yi wa Olakitan fashi da makami a ranar 21 Ga Augusta, 2018, kuma ‘yan sanda sun kama wadanda ake zargi mutum hudu da kama da bindiga a hannun su.

Sai dai kuma lauyan a cikin takardar korafin da ya aika wa Sufeto Janar, ya ce abin takaici, amma ‘yan sanda sun saki wadanda aka kama din, kuma an rasa inda bindigar da aka kama a hannun su ta ke.

Ba a nan maganar ta tsaya ba, lauya Ogunmodede ya ce ‘yan sanda da kuma wadanda ake zargi da yin fashin sun hada baki su na yi wa wanda aka yi wa fashi bi-ta-kulli.

Ya ce ‘yan sanda sun yi masa sharrin wai ya na sojan-gona, har ma suka kama shi, suka gurfanar da shi a kotu.

“‘Yan sanda sun sallami wadanda ake zargi su hudu, Rasaq Lawal, Yemi Richard, Tajudeen Richard da kuma Saka. Sannan kuma bindigar da suka yi wa Olakitan fashi wai ta bace a hannun ‘yan sanda.”

Lauya ya ce bayan ‘yan sanda sun maka wanda ya ke karewa din a kotun, sai alkalin Kotun Majistare ta Ifo ya sallame shi, domin bai same shi d laifin komai ba.

A karshe ya nemi a bi wa wanda ya ke karewa hakkin sa na sakin wadanda ake zargi sun yi masa fashi da kuma gano bindigar da aka yi masa fashin da ita.

An tambayi Kakakin Yada Labarai na ‘Yan Sanda na Kasa, Frank Nba, ya ki magana, domin a cewar sa, bai samu labarin zuwan wasikar ba tukunna.

Share.

game da Author