Kwamiti ya kama sojoji da sarakuna da hannu a kashe-kashen Zamfara

0

Kwamitin da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya kafa domin gano masu hannu a kashe-kashe da garkuwa a Jihar Zamfara, ya mika rahoto ranar Juma’a, inda acikin rahoton ya kama sojoji da sarakunan gargajiya da laifin wajen rikicin.

Kwanan baya ne dai gwamnatin jihar ta kira taron sulhu, domin shawo kan rikice-rikicen da ya dabaibaye jihar sama da shekaru bakwai.

Rahoton Kwamiti

Cikin watan Yuli ne aka kafa kwamiti, a karkashin jagorancin tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Muhammad Abubakar.

An kafa kwamitin domin gano hanyar da za a bi a magance matsalar tsaro a jihar ta Zamfara. Rahoton kwamitin ya nemi a kori wasu jami’an sojoji sannan kuma a tube rawanin wasu sarakunan gargajiya da ake zargi da laifi.

Abubakar ya shaida wa gwamnan cewa “akwai sarakuna biyar da hakimai 33 da dagatai masu tarinnyawa da aka tabbatar da cewa su na da hannu a hare-haren da aka rika kaiwa a jihar Zamfara.”

Sannan kuma kwamitin ya kama wasu jami’an sojoji 10 da laifi, sai kuma wasu jami’an ‘yan sanda da jama’ar gari masu goyon bayan ‘yan bindigar da suka kashe daruruwan jama’a. Sun kuma kone kauyuka, sun sace shanu, abinci, lalata dukiya da kuma karbar bilyoyin kudaden diyya daga wadanda aka yi garkuwa da su.

Da ya ke jawabi, Gwamna Matawalle ya ce zai yi amfani da duk abin da rahoton kwamiti ya bayar da shawara a yi, ba tare da shakka ko tsoron kowa ba.

“Babu ruwa na da kusanci da wani mai hannu a wannan rahoton da aka bayar, kuma in dai an kama ka da laifi, ko babu ruwa na da bangaranci, sko shiyanci ko batun addinin mu daya da mai laifi ko kabila daya. Duk wanda hukuncin ya fada kan sa, to za a hukunta shi.” Inji Gwamna Matawalle.

Daga nan ya ce wadanda kuma doka ba ta ba shi izni ko karfi hukunta su ba, to zai mika na su rahoton ga gwamnatin tarayya domin ta hukunta su.

Da aka tuntubi kakakin Operation Sharan Daji. Oni Orisan, sai ya ce wa PREMIUM TIMES ai ba zai iya magana ba a yanzu, domin rahoton kwamitin bai shiga hannun sa ba.

Daga nan sai Matawalle kuma ya ce zai gana da Shugaba Muhammadu Buhari, domin neman agajin sa wajen kafa Gidauniyar Tallafa wa Marayu da Zawarawa 4,483 wadanda aka kashe mazan su sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.

Share.

game da Author