Kungiyar PCN ya rufe shagunan saida magani 332 a jihar Jigawa

0

Kungiyar masana magungun ta kasa rashen jihar Jigawa (PCN) ya rufe manya da kananan shagunan saida magunguna 332 a fadin jihar.

Darektan sa ido na PCN Anthonia Aruya ta sanar da haka wa manema labarai a garin Dutse ranar Lahadi.

Aruya ta ce kungiyar ya kama wadannan shagunan magunguna ne da laiffukan da suka hada da rashin lasisin bude shago, siyar da magani ba tare da izinin ma’aikacin kiwon lafiya ko kuma masanin magani ba, rashin tsafta, rashin ingantaccen wurin ajiye magani.

“ Mun kai ziyara bazata ga shagunan saida magani 462 a kananan hukumomi 26 daga cikin 27 dake jihar.

“Daga cikin wadannan shaguna mun rufe manyan shaguna biyar da kananan shaguna 327 a fadin jihar.

Aruya ta yi kira ga mutane da su hada hannu da hukumar domin bankado baragurbin shagunan saida magani a jihar.

“Muna kuma mika godiyar mu ga ma’aikatar kiwon lafiya na jihar, jami’an tsaro, masu ruwa da tsaki da gidajen yada labarai bisa nasarar da muka samu a wannan aiki.

Aruya ta ce kungiyar za ta ci gaba da gudanar da bincike domin ganin ta kawar da duk ire-iren wadannan baragurbin shagunan a fadin jihar.

Idan ba a manta ba a watan Yulin da ta gabata ne kungiyar PCN ta rufe manya da kananan shagunan siyar da magani guda 231 a jihar Nasarawa.

Share.

game da Author