Kotun ECOWAS ta ce Najeriya ta biya wani soja diyyar naira miliyan 10

0

Kotun ECOWAS ta umarci Gwamnatin Najeriya ta biya wani soja mai suna Barnabas Eli diyyar naira milyan 10.

Wannan umarni ya biyo bayan korar shi da aka yi ne saboda bindigar da aka damka masa ya na aiki da ita ta bace a hannun sa, a cikin 2012.

Sannan kuma kotun ta umarci a biya shi dukkan albashin sa da sauran hakkokin sa, tun daga watatan Maris, 2015 har zuwa ranar da aka sake shi daga tsarewar da aka yi masa.

Bacewar bindiga a hannun Eli ta janyo masa daurin shekaru biyu a kurkuku, ba tare da sanar wa hukuma cewa an yanke masa hukuncin dokar soja ba.

Da ta ke yanke hunci, Kotun ECOWAS ta yi amfani da Doka ta 90(40) ta ce an tauye wa soja ‘yancin sauraren ba’asin sa a cikin lokaci.

Kotun ECOWAS ta kara jaddada Dokar Soja ta A20, cewa tilas sai an sanar da hukuma wanda aka hukunta a karkashin dokar, wadda ba a yi hakan ba a hukuncin da aka yanke wa sojan.

Kotun ta kara da cewa kama sojan da tsare shi da kuma hukuncin da aka yanke masa duk an yi su a kan ka’ida. Amma inda aka kwafsa shi ne da aka bari ya shekara biyu a tsare ba tare da sanar da hukuma ba ballanatana ta amince da hukuncin da aka yanke masa, kamar yadda dokar soja ta tanadar a rika yi kan duk wanda aka yanke wa hukunci.

A kan haka ne a ranar 11 Ga Oktoba kotun ta yanke hukuncin cewa, ‘tsarewar da aka yi wa sojan a kurkuku karya doka ce aka yi ta Sashe na 6 na Dokar ‘African Charter’.

Sojan dai ya kai kara ne cikin 2016, a shari’a mai lamba ECW/CCJ/APP…/2016, inda ya zayyana cewa cikin 2012 ya na aiki a matsayin san a Sojan Najeriya, sai aka sace bindigar sa a ‘Sector 7, Riyom, Jihar Filato.

Daga nan me aka kama shi, aka tsare, aka yi masa shari’a sannan kuma aka kore shi daga aikin soja.

Eli ya nemi kotu ta bi masa hakkin sa cewa kora da tsarewar da aka yi masa duk haramtattu ne.

A daya bangaren gwamnati dai ba ta musanta ko yin ja-in-ja da wannan hukunci ba a lokacin yanke wannan hukunci.

Alkalan da suka yanke wannan hukunci sun hada da: Gberi-Be Outtara, wanda shi ne shugaba, Dupe Atoki da Januaria Costa.

Share.

game da Author