Kotu ta tsige Sanata da Dan Majalisar APC na Sokoto, ta maye su da ‘yan PDP

0

A ranar Laraba ne Kotun Daukaka Kara ta tsige Sanata Abubakar Shehu Tambuwal na APC, ta maye gurbin sa da dan takarar sanata na PDP, Ibrahim Danbaba.

Haka kuma kotun duk a yau ta tsige Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Bodinga, Dange-Shuni da Tureta, na APC, ta maye gurbin sa da Balarabe Kakale na PDP.

Da ya ke jawabin yanke hukunci, Babban Mai Shari’a, Frederick Oho, ya yi watsi da hukuncin da Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta yanke, wadda ta bai wa wadanda aka tsige din gaskiya a lokacin.

Tun da farko dai Danbaba da Kakale na PDP sun kai kara, inda ba su yi nasara ba a Kotun Sauraren Kararrakin Zabe.

Sun kara daukaka kara ne saboda rashin gamsuwa da hukuncin. Amma a yau sun yi nasara, inda Mai Shari’a ya umarci sanata da wakilin tarayya na APC su sauka, na PDP su maye gurabun su.

Har ila yau, a jiya Talata ne kuma kotun ta bada umarnin cewa a sake zaben dan Majalisa a Karamar Hukumar Sokoto ta Arewa.

Share.

game da Author