Kotu ta bada umarin rufe asusun bankuna 45 mallakar masu sumogal din shinkafa

0

Babbar Kotun Tarayya reshen Abuja, ta bada umarnin a rufe asusun bankuna har 45 mallakar wasu kamfanoni uku da ake zargin na da hannu wajen fasa-kwaurin shinkafa cikin kasar nan.

Kamfanonin da aka rike asusun ajiyar bankunan na su sun hada da Sun Sam A1 International Limited, Sam Sun International Limited da kuma Sunchrist O. Trans Nigeria Limited. An bada umarni ruke asusun su da ke cikin bankunan First Bank, Stanbic IBTC, Union Bank, UBA, Zenith Bank, Sterling Bank, Access Bank, FCMB, Polaris Bank da kuma Eco Bank.

Mai Shari’a Mohammed Ahmed ya umarci hedikwatar kowane banki daga cikin bankunan 10 cewa kada su kuskura su bari a yi wata hada-hada a wadannan asusu, har nan da kwanaki 45.

Kotu ta ce asusun guda 45 za su ci gaba da kasancewa a rufe, har zuwa lokacin da Babban Bankin Najeriya (CBN) zai kammala binciken sa.

Lauyan CBN Nosike Nicholas ya nemi kotun ta bada umarnin kulle asusun guda 45 tsawon kwanaki 90. Sai dai kuma Mai shari’a ya amince da kwanaki 45 kawai.

Alkali ya ce ya bayar da kwanaki 45 ne. Amma idan har kwanakin suka cika ba tare da CBN ya kammala binciken sa ba, to za a iya kara wani wa’adin ci gaba da kulle asusun idan CBN ya nemi karin wa’adin.

Lauya Nosike ya ce CBN na ci gaba da bincike a kan asusun ajiyar kamfanonin uku. Sannan kuma irin hada-hadar da su ke yi za ta ita gurgunta shirin noman shinkafa a kasar nan da kuma tattalin arzikin kasar shi kan sa.

Share.

game da Author