Kotun dake Ikeja jihar Legas ta tsare wani magidanci mai suna Chinedu Ifeteka mai shekaru 46 da ta kama da laifin yi wa ‘yar cikinsa mai shekaru 14 fyade.
Ifeteka wanda ke da sana’ar siyar da kaya a kasuwar Ojo ya musanta aikata haka.
Alkalin kotun B.O. Osunsanmi ta bada belin Ifeteka akan Naira 300,000 tare da gabatar da shaidu biyu dake biyan haraji ga gwamnatin jihar Legas.
Lauyan da ya shigar da karan Ezekiel Ayorinde ya bayyana cewa Ifeteka ya fara yin lalata da ‘yarsa tun a ranar 9 ga watan Agusta a gidan su dake Ojo.
Ya ce Ifeteka kan danne ‘yar sa mai shekaru 14 a duk lokacin da matarsa bata nan a gida.
“Da yarinyar ta gaji da abin da mahaifinta yake yi mata sai ta fadi wa mahaifiyarta inda daga nan ne jami’an tsaro suka samu labari.
Ayorinde yace bisa ga doka hukuncin duk wanda aka kama da laifin aikata haka shine daurin rai da rai a kurkuku.
Za a ci gaba da shari’ar ranar 25 ga watan Nuwamba.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta damke wani mai suna Innocent Ifunayachi mai shekaru 34 da laifin yi wa ‘yar shekara 14 fyade.