KIN BIYAN BASHI: RIFAN za ta maka manoman shinkafa ‘yan jihar Katsina 113 a kotu

0

Kungiyar manoman shinkafa na Najeriya reshen jihar Katsina (RIFAN)ta ce za ta maka manoman shinkafa 113 da suka ki biyan bashin kudade da kayan noman da shirin ‘Anchors Borrowers Program’ ya basu.

Shugaban kungiyar dake karamar hukumar Daura Nura Baure ya fadi haka da yake hira ga Kamfanin Dillancin labaran Najeriya a garin Daura ranar Talata.

Baure yace RIFAN za ta dauki wannan mataki ne ganin cewa manoman da suka karbi bashin kayan noma sun ki biya duk da tsawon lokacin da aka ba su domin su maido da kudaden.

Ya ce daga yanzu kungiyar za ta dauki mataki mai tsauri akan duk manomin da ya karbi kayan noma kuma ya ki biya.

“Dama gwamnati ta tsara wannan shiri ne domin tallafa wa manoma a jihar yadda za su iya karban bashin kayan noma sannan su biya bayan shekara daya.

Baure ya kara da cewa kungiyan ya raba irin shinkafa, takin zamani, goran feshi, maganin feshi, injin din banruwa da sauran su ga manonan. Saidai kuma duk da haka ya yabawa wasu manoman da suka iya yin karfin hali suka biya basukan ada suka karba.

Akalla noma 5000 ne suka yi rajista da wannan kungiya domin samun tallafi inda a karon farko kungiyar ta tallafa wa manoma 3,500.

Sannan a kwanakin baya kungiyar ta tallafa wa manoman ridi wajen siyar da ridin da suka noma a kasuwa.

Share.

game da Author