KETA ALKUR’ANI: Matawalle yayi Kira da a tashi yi azumi da addu’o’I

0

Gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga mutanen jihar da su yi azumi da addu’o’I na tsawon kwanaki uku domin Allah ya tona asirin da wadanda suka kekketa Al’Kur’ani a jihar.

Gwamnan jihar Bello Matawalle ya yi wannan kira ne ranar Juma’a a wani takarda da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Yusuf Idris ya saka wa hannu.

Idris ya ce gwamnati ta sanar da haka ne bayan sauraran shawarwari daga kungiyoyin Musulunci dake jihar.

“Tun a shekarar 2016 gwamnati ke fama da matsalolin rashin daraja Al’Kurani mai girma da mutane ke yi a jihar musamman a babbar birnin jihar wato Gusau.

“A dalilin haka muke kira ga mutane da su gudanar da azumi da addu’o’I domin Allah ya ladabtar da mutanen dake aikata wannan mummunar aiki a jihar.

Matawalle ya yi kira ga limamai a duk masallatan jihar da su yi addu’o’I na musamman tare da yin wa’azi domin tunatar da mutane laifin yin haka.

Idan ba a manta ba a mankon da ya gabata ne aka tsinci fallayen Al’kur’ani mai girma a kwatamin wata makarantar firamare maisuna makarantar Shattima dake Gusau a jihar.

A dalilin haka gwamnan jihar Bello Matawalle ya bada umurin rufe wannan makaranta tare da dakatar da malaman dake aiki a makarantar.

Gwamnati ta ce za ta biya Naira miliyan biyu ga duk wanda ke da bayanai akan wanda ko wadanda suka aikata wannan mummunar aiki a jihar.

Share.

game da Author