Shugaban kungiyar kare mutuncin masu fama da cutar kanjamau a Najeriya (COCSHAN) Ikenna Nwakamma ya yi kira ga gwamnatocin jihohin kasar nan, kananan hukumomi da masu fada a ji a fannin kiwon lafiya da su hada hannu domin dakile yaduwar cutar kanjamau a kasar nan.
Nwakamma ya fadi haka ne da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja ranar Litini.
Ya ce abun takaici ne yadda bayan shekaru 20 Najeriya na nan jiya iyau a maganar yaki da cutar kanjamau daga kasar nan duk da dimbin tallafi da me shigowa daga kungiyoyin kasashen waje.
Nwakamma ya ce kamata ya yi gwamnatocin jihohin kasar nan su gane cewa suna da mahimmiyar rawan da za su rika takawa wajen inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan.
“A mai makon biya wa mutane kujerun Makka da Jerusalem kamata ya yi gwamnatocin jihohin kasar nan su yi amfani da wadannan kudade wajen inganta kiwon lafiyar mutanen su ne.
Ya ce ware isassun kudade, kafa inshoran kiwon lafiya, mara wa fannin bincike da sarrafa magunguna baya da tallafa musu, samar da dokoki da zasu k
taimaka wajen dakile yaduwar cutar na daga cikin hanyoyin da ya kamata a maida da hankali a kai.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne Nwakamma ya bayyana cewa har yanzu dai masana’antun sarrafa magunguna a Najeriya basu fara sarrafa maganin kawar da cutar kanjamau ba cewa haka na da nasaba ne da rashin samun izinin sarrafa maganin daga gwamnati.
Discussion about this post