Katsinawa 23 da aka sayar a Burkina Fasso sun bayyana azabar da suka sha

0

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana ceto wasu Katsinawa 23 da aka ribbata, aka sayar da su a kasar Burkina Faso.

Gwamnan jihar, Aminu Masari ne bayan samun labarin su, nan da nan ya aika da jami’in da zai je ya dawo da su.

Da ya ke magana bayan ya samu nasarar dawowa da su, a Gidan Gwamnatin Katsina, Mashawarcin Gwamna a Fannin Dakile Tu’ammali da Kwayoyi, Hamza Borodo, ya ce Jakadar Najeriya a kasar Burkina Fasso ce, Ramatu Mohammed ta aiko wa Gwamna Masari wasika, bayan ta samu labarin halin da Katsinawan ke ciki.

Ya ce sai dai kuma yayin da ya isa kasar domin ya dawo da su Najeriya, biyu sun ki dawowa, sun ce babu su babu dawowa Najeriya.

Ya ce bincike ya nuna mutane biyu din da suka ki dawowa, su ne dillalan wata mata wadda ke sayen mutanen ta na saka su a kangin bauta.

Daga cikin wadanda suka ki dawowa din har da mai suna Usman Wagini, wanda cikin wadanda aka ceto din mai suna Usman Sulaiman ya ce Wagini din ne yq je har kauyen su a Kankara, ya yi musu romon-kunne cewa za a kai su kasar da za su je su yi aiki su na samun kudi birjik.

“Da farko Legas aka nufa da mu. Daga nan sai Kwatano dai Togo. An sayar da mu ga wata mata, wadda sai daga baya muka gane kawai aikin bauta mu ke yi a kasar.

“Babu abincin kirki, kuma babu ruwan sha wadatacce. Idan ba ka lafiya, sai dai kara hakura, ka yi ta addu’ar samun sauki kawai.”

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES HAUSA cikin watannin baya ta buga wata hira da Jakada Ramatu, inda ta bada labarin cewa akwai ‘yan mata masu karuwanci a Burkina Fasso daga Najeriya sama da dubbai.

Ta ce duk a cikin kauyuka da surkukin daji su ke karuwancin, a sansanonin karti masu hakar ma’adinai.

Share.

game da Author