KASAFIN 2020: Kashi 1 bisa 4 na kasafin zai kare a biyan basussuka

0

Kashi 1 bisa 4 idan aka raba kasafin 2020, duk a wajen biyan basshi zai tafi. Haka jawabin da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar ya tabbatar.

Buhari ya ce daga cikin kasafin na naira tiriliyan 9.75, naira tiriliyan 2.45 duk wajen biyan basussuka na cikin gida da kuma na waje za su tafi.

Kasafin kenan ya nuna akwai tsarin biyan-bashin-daddawar-kauye. Domin Buhari ya ce an samu gibi a shi wannan na 2020, har na naira tiriliyan 2.18.

Wadannan kudaden gibi kuwa Buhari ya ce ranto wasu kudin za a sake yi a cike wawakeken gibin da su.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana samun gibi a Kasafin 2020 da ya gabatar yau a Majalisa, har na naira tiriliyan 2.18.

Da ya ke jawabi, Buhari ya ce sai dai kuma gibin bai kai kashi 3% da dokar kasafin kudi ta ce ba ta yarda a samu ba.

Buhari ya ce za a cike wannan wawakeken gibi da basussukan da za a ciwo a nan cikin gida da kuma waje.

BIYAN BASHI

Dangane da ci gaba da biyan basussuka da Najeriya ke yi, Buhari ya ce za a biya har naira tiriliyan 2.45 a cikin kasafin 2020. Sannan kuma ya ce gwamnatin tarayya za ta bada karfi wajen ramcen kudade daga tsarin Sukuk, Green Bonds da Diaspora Bonds.

Da ya waiwaya kan kasafin 2019 da ya gabata, Buhari ya ce an samu nasarar rage hauhawar farashi da tsadar rayuwa daga kashi 18.17 cikin 2017, zuwa 11.02 a karshen Agusta, 2019.

Ya kuma bugi kirjin cewa asusun ajiyar dukiyar Najeriya a waje ya karu daga dala bilyan 23 cikin 2016 zuwa dala bilyan 42.5 cikin Augusta, 2019.

HARAJIN VAT

Buhari ya ce an kara harajin VAT daga kashi 5% zuwa 7.5% domin a yi amfani da kudaden wajen inganta lafiya, ilmi, kayan more rayuwa, inda jihohi da kananan hukumomi za su rika kwasar kaso 85% na kudaden.

Buhari ya ce ba za a karbi harajin VAT daga magunguna, littattafai, kayan masarufi da sauran su ba.

Share.

game da Author