KASAFIN 2020: Buhari ya zabtare kashi 94% na kudaden Shirin Inganta Rayuwar Al’umma (SIP)

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya yanke kashi 94% na yawan kudaden da suka kamata a kashe wajen Shirin Inganta Rayuwar Al’umma, wanda a Turance aka fi sani da ‘Social Intervention Programmes’.

Yayin da a kasafin kudin 2017, na 2018 da na 2019 duk aka ware wa SIP naira biliyan 500, a wannan kasafi na 2019 kuwa naira biliyan 30 kacal aka ware wa shirin.

Haka dai ya ke a kididdige a cikin jadawalin alkaluman adadin kudaden kasafin 2020 da Buhari ya gabatar wa Majalisa a ranar Talata da ta gabata.

Wannan shiri ya fada cikin ce-ce-ku-ce a kwanan baya, biyo bayan batun da ya taso na cire shirin daga Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, inda a can ake kula da shirin tun daga lokacin da aka kirkiro shi cikin 2026. A yanzu Buhari ya yi bayanin maida shirin a karkashin sabuwar Ma’aikatar Ayyukan Jinkai da Harkokin Inganta Rayuwar Jama’a.

Sauran shirye-shiryen da ke karkashin SIP sun hada da N-Power, Shirin Ciyar Dalibai, Shirin Tallafin Kudade Kai-tsaye da kuma Shirin Tallafawa ga Masu Kananan Sana’o’i.

Cikin watan Mayu da ya gabata ne Shugabar Mashawarciyar Shugaba Buhari kan Inganta Rayuwar Jama’a, Maryam Uwais ta bayyana cewa a cikin shekara uku, wannan shiri ya karbi naira biliyan 470.825 daga cikin naira tiriliyan 1.5 da aka ce za a kashe masa a cikin shekaru uku.

Hakan kenan ya na nuni da cewa kashi daya bisa uku (ko kuma kasa da hakan) ne kadai gwamnatin tarayya ta fitar kuma ta kashe a shekaru uku da suka gabata.

Wato tunda Buhari ya kara zabtare kasafin zuwa naira bilyan 30, duk da haka adadin kudin bai kai na yadda aka rika kashewa a duk shekara a shekaru uku da suka gabata ba, inda aka rika kashe naira bilyan 157 kacal, maimakon naira bilyan 500, kamar yadda ya ke a kasafin 2017, 2018 da 2019.

Ba a dai san dalilin da ya sa Buhari ya yi wannan wawakeken yanke kasafin kudaden Shirin Ayyukan Inganta Rayuwar Al’umma, na SIP daga naira biliyan 500 zuwa naira biliyan 30 ba.

Kokarin jin ta bakin Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa, Femi Adesina, bai yi nasara ba, domin cewa ya yi wannan batu ai Ma’aikatar Kudade ce ya kamata a tuntuba, ba Fadar Shugaban Kasa ba.

An yi kokarin jin ta bakin Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed, amma ba ta dauki waya ba, kuma har yanzu ba ta maido amsar sakon tes din da aka tura ma ta ba.

Share.

game da Author