Ministan Kwadago da Inganta Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Chris Ngige, ya bayyana cewa babu yadda za a yi Gwamnatin Tarayya ta iya dorewa da biyan albashi kamar yadda Kungiyar Kwadago ke bukata, har sai an rage ma’aikata tukunna.
Ngige ya ce gwamnatin tarayya na bukatar karin kudi zunzurutu har naira bilyan 580 domin biyan karin albashi.
Tun dai cikin watan Afrilu ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa dokar karin albashi hannu, amma ga shi wata bakwai kenan bayan da Majalisar Tarayya ta mika masa kudirin, ba a fara biya ba.
Kafin nan kuma an rika sukar Majalisa cewa jinkirin ta ne wajen mika wa Buhari kudirin domin ya zama doka ya sa ba a fara aiki da sabon tsarin albashin ba.
Ngige wa yi furucin batun rage ma’aikata ne a lokacin da wani reshe na shugabannin kungiyoyin Kwadago ya kai masa zuwa ziyara a ofishin sa, jiya Alhamis.
Ya ce tuni gwamnati ke ta kokarin kauce wa batun rage ma’aikata kafin ta samu ta iya biyan albashi.
Don haka ya ce ya kamata kungiyoyin Kwadago da ma’aikata su hakura da adadin tayin karin da gwamnatin tarayya ta ce za ta iya yi kawai.
A cewar sa, ya kamata a amince da tayin gwamnari, a wuce wurin kawai, domin saura watanni uku a fara amfani da karin ka’in-da-na’in.
Daga nan sai ya kara da cewa a gaskiya gwamnati ba za ta iya alkawarin biyan abin da ta san ba ta za iya biya ba.
Ngige ya ce an fara biyan masu albashi daga mataki na 01 zuwa 06.
Ita dai gwamnati cewa ta yi za ta iya biyan karin kashi 9.5 bisa 100 na albashin masu mataki na 07 zuwa 14. Sai kashi 5 bisa 100 na masu matakin albashi daga 15 zuwa 17.
Ita kuma Kungiyar Kwadago ta cirje cewa sai dai a yi karin kashi 30 bisa 100 ga masu matakin albashi na 07 zuwa 14. Kamar yadda aka yi wa masu 01 zuwa 06 karin kashi 30 bisa 100.
Su kuma masu mataki na 15 zuwa na 17, to NLC ta ce sai dai a yi masu karin kashi 25 bisa 100, ba 5 bisa 100 kamar yadda gwamnati ta ce za ta iya yi kadai ba.