KARANBAU: Yara uku cikin 10 na kamuwa da cutar a duniya – WHO

0

Sakamakon binciken da Kungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya ta gudanar ya nuna cewa yara uku cikin 10 na kamuwa da cutar karanbau a duniya.

Binciken wanda WHO ta gudanar tare da hadin guiwar hukumar hana yaduwar cututtuka na kasar Amurka (CDC) ya nuna cewa duk shekara akan haifi jarirai 100,000 dauke da wannan cuta a duniya.

WHO ta bayyana cewa hakan na da nasaba ne da rashin maida hankali wajen yin allurar rigakafi ga yara da mata masu ciki.

Bincike ya nuna cewa kasashen duniya 80 ne suka yi nasarar rabuwa da wannan cuta kuma har yanzu kasashen masu tasowa musamman a Afrika na nan na fama da yaduwar cututtuka.

A yanzu haka Najeriya na daya daga cikin kasashen Afrika 26 dake fama da matsalolin da suka shafi rashi ko kuma karancin allurar rigakafin wannan cuta.

A dalilin haka ya sa yara da manya ke kamuwa da cutar.

Shugaban sashen yiwa yara allurar rigakafi na hukumar WHO Kate O’Brien ta ce Najeriya da sauran kasashen Afrika za su iya rabuwa da wannan cuta ne idan gwamnati ta samar da isassun maganin rigakafi sannan da inganta fannin kiwon lafiya a kasashen su.

O’Brien ta yi kira ga kasashen da suka rabu da cutar da su ci gaba da yi wa yara da mata masu ciki allurar rigakafi cewa yin haka zai taimaka wajen hana yaduwar cutar a duniya.

Karanbau

1. Karanbau cuta ce dake kama yara da manyan musamman mata masu ciki.

2. Yin allurar rigakafin cutar ne hanyar samun kariya daga kamuwa da cutar.

3. Jaririn dake cikin mahaifiyar sa na iya kamuwa da cutar idan har mahaifiyar bata yi allurar rigakafi ba.

4. Karanbau na sa yaro ya zama kurma,yana sa a kamu da makanta, cututtukan dake kama zuciya da sauran su a jikin yara.

5. Mace mai ciki za ta iya yin bari, haiho dan da bashi da rai ko kuma dan dake da nakasa a jikinsa a dalilin kamuwa da cutar.

6. Kamata ya yi mace ta yi allurar rigakafin cutar kafin ta dauki ciki kokuma a lokacin da cikin ke wata uku

7. Alamun cutar sun hada da zazzabi,rashin iya cin abinci,yawan kuka ga yara,kurarraji a jiki da sauran su.

8. Ana iya kamuwa da cutar idan mai dauke da ita ya yi tari ko kuma ruwan dake fita daga kurarrajin ya tabi jikin mutum.

9. Ana iya gane alamun cutar ne idan kwayoyin cutar sun yi kwanaki 16 zuwa 18 a jikin mutum.

10. Rashin gaggauta kai mai dauke da cutar asibiti na iya yin ajalinsa.

Share.

game da Author