KANO: Kotu ta bada belin malamin da ke karbar kudi wajen daliban sa don cin jarabawa

0

A ranar Talata ne kotu a jihar Kano ta gurfanar da wani malamin Kwalejin Kimiyya Da Fasaha dake jihar Aminu Chedi da ake yi zargin yana karbar kudi wajen daliban sa domin su ci jarabawa.

Alkalin kotun Muhammad Idris ya bada belin Chedi a kan Naira 100,000 tare da gabatar da shaidu biyu.

Za a ci gaba da shari’ar ne ranar 15 ga watan Oktoba.

Dan sandan da ya shigar da wannan kara, Badamasi Gawuna ya bayyana cewa a ranar Tara ga watan Agusta 2019 wannan malami Chedi ya umurci wani tsohon dalibin kwalejin dake taimaka masa da aiyukka mai suna Jibrin da ya karbi Naira 1,000 daga hannun daliban sa.

Gawuna ya ce sun gano cewa Jibrin zai karbi wadannan kudade ne domin taimaka wa daliban ajin cin jarabawar darasin Turanci.

“Jibrin ya karbi Naira 11,200 daga hannun dalibai.

Ya ce har yanzu dai jami’an tsaro na farautan Jibrin da ya cika wa wandonsa iska ya tsere.

Sai dai kuma malamin wato, Chedi ya musanta aikata haka a kotu.

Share.

game da Author