KANO: Jami’an Hisbah sun kubutar da yara 36 dake tsare a gidan Kangararru

0

Jami’an gwamnatin jihar Kano tare da ma’aikatan hukumar hisbah sun kubutar da yara 36 dake tsare a gidan kangararru dake jihar Kano.

Gwamnati ta far wa wannan gida ne da ake hora yara kangararru dake kwatas din Daiba, Rijiyar Lemu dake karamar hukumar Dala ranar Laraba da yamma.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike kan aiyukkan gidajen ladabtar da kangararrun yara a jihar domin taka musu burki.

Bayan haka PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda masu gidajen irin haka suka fara rufe gidajen su domin gudun fadawa hannun gwamnati.

Da yake bada sanarwa a Rediyon Freedom shugaban kwamitin Muhammed Tahar ya bayyana cewa shi mai wannan gidan kangararru ya yi kaurin suna wajen bude gidaje irin haka a jihar.

Tahar ya yi kira ga duk iyayen da ‘ya’yan su ke wadannan gidaje da su hanzarta zuwa ofishin Hisba domin tafiya dasu.

Idan ba a manta ba a cikin watan nan na Oktoba ne Hukumar tsaro na ‘Sibul Difens’ NSCDC ta kubutar da mutane 11 dake tsare a wasu gidajen kangararru biyu a Zariya jihar Kaduna.

Jami’an tsaron NSCDC sun far wa wadannan gidaje biyu a Limanchi Corner da Marmara inda suka iske wadannan mutane masu shekaru 11 zuwa 40 daure cikin ankwa.

Kafin hakan mai rikon kujerar gwamnan jihar Kaduna, mataimakiyar gwamnan jihar Hadiza Balarabe ta jagoranci jami’an ‘yan sanda zuwa wani gidan kangararru da ke Rigasa, inda suka kubutar da wasu mutane da mafi yawan su matasa ne har 147.

Share.

game da Author