KANJAMAU: Kashe mutane Abakala ya rika yi, ba basu magani ba – Farouk

0

Mohammed Farouk, daya ne daga cikin wasu sojoji 30 da aka tabbatar sun kamu da cutar Kanjamau bayan dawowa daga aikin samar da zamar Lafiya na rundunar ECOMOG, ya karyata Dokta Jeremiah Abalaka da ya rika cewa ya na da maganin warkar da cutar.

Farouk ya ce a shekarar 1999 zuwa 2000 Dakta Abalaka ya fito ya rika cewa wai yana da maganin warkar da Kanjamau. Tun bayan fadin haka sai hukumar Rundunar Sojin Najeriya ta kwashe su, su 30 aka mika wa Dakta Abalaka domin yayi musu magani.

Farouk ya kara da cewa wannan likita da yake kiran kansa mai maganin Kanjamau, wato Abalaka shirga karya yake ta yi wa mutane. Kashe mutane kawai yake yi da sunan wai yana yi musu magani.

“ Mu 30 ne aka kaimu wurin likita Abalaka domin yayi mana magani amma a yanzu haka da nake yi muku magana, 29 duk sun mutu saura ni kadai ne ban mutu ba kuma ma a yanzu haka ina dauke da cutar Hepatitis B.

Farouk ya yi kira ga wadanda ke fama da Kanjamau da su rika zuwa asibitoci suna karbar magani. Yana mai cewa hakan shine ya fi musu ba bin irin su Abalaka ba.

Shi dai Likita Abalaka ya dade ya na shela wa mutane da gwamnati da su garzayo wurin sa domin samun maganin Kanjamau da wasu manyan cututtuka da akan yi fama da su musamman a kasar nan.

Abalaka ya ce shine kadai yake da maganin Kanjamau na gaskiya da idan mai ita ya sha zai warke daga cutar. Ya rika yada manufofin sa da tallata maganinsa a kafafen yada labarai.

Wannan kuranta maganin sa da ya ke ta yi ne ya sa a aka mika masa wasu sojoji 30 da suka kamu da cutan Kanjamau.

Daya daga cikin su da aka ambato a farkon wannan labari Farouk ya karyata Likita Abalaka inda ya ce kasurgumin makaryace ne sannan kisan mutane kawai yake yi da sunana wai yana yi musu magani.

Share.

game da Author