Jami’ar gwamnati kasar Amurka Claire Pierangelo ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta samar da kula kyauta wa mutanen dake fama da cutar Kanjamau cewa yin haka zai taimaka wajen dakile yaduwar ta.
Pierangelo ta bayyana haka ne a taron gabatar da gudunmawar kasar Amurka don kula da mutane 23,000 dake dauke da Kanjamau kuma basu da halin iya siyan magani daga nan zuwa watan Satumba 2020.
Idan ba a manta ba shirin tallafa wa mutane dake dauke da kanjamau dake Amurka wato PEPFAR ta amince ta kara yawan kudade domin kula da masu fama da kanjamau a Najeriya.
Zai dai wannan karon PEPFAR ta ce za ta yi amfani da wannan tallafi ne domin kula da mutane 500,000 dake dauke da cutar a jihohin Enugu, Akwa-Ibom da Ribas.
“ 500,000 din da PEPFAR ta amince ta kula da su kari ne kan mutane 700,000 dake samun kula daga kanjamau a Najeriya.
Bayan haka Pierangelo ta kuma yi kira ga gwamnati da ta samar da kula kyauta ga mata masu ciki dake dauke da kanjamau.
“ Hakan na nufin cewa duk wani taimakao da gwamnati za ta iya yi shine idan da hana a karbi kudade wajen mutanen dake fama da kanjamau a asibitocin kasan.
Idan ba a manta ba hukumar hana yaduwar cutar Kanjamau ta kasa (NACA) ta bayyana cewa mutane miliyan 1.9 ne ke dauke da cutar a Najeriya.