Kada a biya ma’aikacin da ba a tantance albashin watan Oktoba – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa daga 31 ga Oktoba, kada a kuskura a kara biyan ma’aikata albashi ba bisa tsarin tantance ma’aikata na IPPIS ba.

Buhari ya ce duk jami’i ko ma’aukatar da ta kuskura ta karya wannan umarni, to zai yaba wa aya zaki.

Ya yi wannan gargadin ne yayin da ya ke jawabin bayyana kasafin kudi na 2020 a zauren Majalisar Tarayya.

Ya ce gwamnati ta fito da tsarin tantance adadin ma’aikata na IPPIS domin ta rika ririta kudade tare da sa-ido kan kudaden da ake kashewa.

Baya ga wannan kuma, Buhari ya sake yin gargadi cewa an rufe kofar daukar ma’aikata a hukumomin gwamnatin tarayya ba tare da an nemi izni ba.

Ya ce za a hukunta duk wanda ya kuskura ya dauki ma’aikata aiki ba tare da ya nemi izni, an amince ya dauka ba.

Ya ce ma’aikatun gwamnati za su kashe naira bilyan 400 wajen gudanar da ayyukan yau da kullum. Ciki kuwa har da sabbin ma’aikatun da gwamnatin tarayya ta kirkiro.

Sai kuma ya yi kira ga dukkan ma’aikatun su rika taka-tsantsan wajen kashe kudaden su.

Kashi 1 bisa 4 na kasafin zai kare a biyan basussuka

Kashi 1 bisa 4 idan aka raba kasafin 2020, duk a wajen biyan basshi zai tafi. Hada jawabi da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar ya tabbatar.

Buhari ya ce daga cikin kasadin na naira tiriliyan 9.75, naira tiriliyan 2.45 duk wajen biyan basussuka na cikin gida da kuma na waje za su tafi.

Kasafin kenan ya nuna akwai tsarin biyan-bashin-daddawar-kauye. Domin Buhari ya ce an samu gibi a shi wannan na 2020, har na naira tiriliyan 2.18.

Wadannan kudaden gibi kuwa Buhari ya ce ramto wasu kudin za a sake yi a cike wawakeken gibin da su.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana samun gibi a Kasafin 2020 da ya gabatar yau a Majalisa, har na naira tiriliyan 2.18.

Da ya ke jawabi, Buhari ya ce sai dai kuma gibin bai kai kashi 3% da dokar kasafin kudi ta ce ba ta yarda a samu ba.

Buhari ya ce za a cike wannan wawakeken gibi da basussukan da za a ciwo a nan cikin gida da kuma waje.

Share.

game da Author