Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa akwai kari wasu taragai 20 da ke kan nhanyar isowa Najeriya, nan da makonni shida daga kasar Chana.
Taragan a cewar Amaechi, za a kai 10 a hanyar jirgin kasa ta Abuja zuwa Kaduna da kuma sauran 10 a hanyar jirgin kasan Lagos zuwa Ibadan, domin a rage cinkoson matafiya.
Ministan ya yi wannan jawabin ne ga manema labarai a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja, jim kadan bayan saukar sa daga kasar Chana.
Wata sanarwa daga Ma’aikatar Sufuri ta bayyana cewa Amaechi ya kai ziyara Chana domin kawo sabbin jirage da kuma karo wasu taragai.
“Duk akwai su a kasa. Amma za a dauki makonni shida kafin ka kawo su Najeriya.”, ijni Ministan, wanda ya ce da zaran an kawo su, za a dauki ‘yan kwanaki kadan wajen kai su Lagos a hada su da kuma kaiwa Abuja can ma a hada su, a rika zirga-zirga da su tsakanin Abuja zuwa Kaduna.
Sai dai ya ce kwanaki biyu kawai za a iya yi a kai na Lagos idan an sauke su a ruwa. Amma na Abuja sai sun dauki mako daya ko fiye da haka.
Ya ce taragan 20 ne, amma za a kai guda 10 Abuja, 10 kuma Lagos zuwa Abuja.
Amaechi ya ce wannan kokari da gwamnati ta yi na dan wani lokaci ne, domin magance matsalar cinkoson fasinjoji.
Amma da zaran an kammala titin jirgi na Lagos zuwa Ibadan, to za a kawo jiragen da ke can Chana.
Ya ce har shigar wasu ma ya yi a can an dana shi, ya ji yadda ingancin su ya ke.
Matafiya daga Abuja zuwa Kaduna, Sokoto, Zamfara, Kano da sauran jihohin Arewa na ci gaba da kaurace wa hanyar Abuja zuwa Kaduna, saboda yawaitar garkuwa da mutane.
Wannan ne ya haifar da cinkoson fasinjoji a tashoshin jiragen kasa da ke Abuja da kuma ta Kaduna.