Ganin cewa saura kwanaki uku kacal suka rage wa’adin da Kungiyar Kwadago ta bai wa Gwamnatin Tarayya domin a yi zaman sulhun karkare kudin karin mafi kankantar albashi, shugabannin kungiyar sun yi barazanar tafiyar yajin aikin game-gari.
Kungiyar wato NLC, ya fara yi wa dukkan ma’aikata shelar shirin tafiya yajin aikin da suka ce zai tsaida komai cak a kasar nan, matsawar nan da ranar 16 Ga Oktoba ba a yi wannan zama ba, tsakanin NLC din da Gwamnatin Tarayya.
NLC ta sanar wa dukkan rassan ta na kowace jiha su yi shirin tafiya yajin aiki.
Dukkan kungiyoyin ma’aikata a karkashin uwar kungiya ta kasa baki daya, wato NLC sun ce matsawar nan da ranar 15 Ga Oktoba ba a yi zaman cimma matsayar adadin karin albashin matakan albashin da ake ta tankiya a kai ba, to kada kowane ma’aikaci ya kara zuwa wurin aikin sa.
Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago sun sha zaman tattaunawa domin kokarin warware tankiyar da ke tattare da batun karin albashi, amma ana tashi baram-baram.
Ko ranar Laraba da ta gabata sai da aka yi zaman, amma aka tashi ba tare da an cimma wata matsayar da kowa ya gamsu da ita ba.
Bayan tashi daga zaman sulhun ranar Laraba wanda bai haifi wani da main ido ba, sai aka amince cewa za a sake zaunawa a ranar Talata, 15 Ga Oktoba.
Duk da cewa an amince za a sake zaunawa a ranar Talata mai zuwa, tuni kungiyoyin kwadago sun shirya tsaf domin fara yajin aiki, matasawar a ranar Talata din babu wani abin da ya wakana da za su amince da shi daga bangaren gwamnatin tarayya.
Babban Sakataren Hada-ka na Kwamitin Tattaunawa kan Karin Albashi, Alade Lawal, ya bayyana cewa shiri ya kankama domin fara yajin aiki a ranar 16 Ga Oktoba, wato Laraba mai suwa .
Ya yi tir da tsarin da gwamnatin tarayya ta yi na raba hankalin ma’aikata, inda ta yi wa ma’aikata masu matakin albashi daga 01 zuwa 06 kari daidai da daidai, su kuma masu mataki na 07 zuwa sama, ake ta yi musu walle-walle.