JIGAWA: An samu rahoton kwararar bakin makiyaya dauke da muggan makamai

0

Al’ummar yankin Karamar Hukumar Miga cikin Jihar Jigawa, su na cikin halin zaman zullumin kwararar bakin makiyaya, wadanda aka yi zargin cewa kuma dauke su ke da muggan makamai tare da dabbobin na su.

An kuma samu rahoton cewa makiyayan sun banka dabbobin su cikin gonakin shinkafa da na dawa, inda suka lalata tare da cinye amfanin gonaki 18.

Sakataren mulki na Karamar Hukumar Miga, Kawu Magaji ya tabbatar da wannan rahoto, inda kuma ya kara da cewa abin damuwa ne matuka. Ya ce makiyayan sun mamaye yankin Miga ne, bayan sun gudo daga yankin Hadejia, inda suka yi rikici tsakanin su da manoman yankin.

Ana zargin wadannan bakin makiyaya daga Jamhuriyar Nijar su ka kwararo cikin Jihar Jigawa.

An kuma ce an tura jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda da sauran su domin su shawo kan makiyayan tare da kauce ci gaba da barnata amfanin gona da kuma hana barkewar rikici.

Hakimin Miga, Mohammed Garba ya tabbatar da wannan hali da ake ciki, wanda ya ce al’ummar Masarautar Miga na zaman dar-dar
Shi kuma Kakakin Yada Labarai na Rundunar ‘Yan Sandan Jigawa, Abdul Jinjiri, ya shaida cewa har zuwa lokacin rubuta wannan labari, bai samu rahoton ba.

Share.

game da Author