Jami’an NSCDC sun kubutar da mutane 11 dake tsare a gidan kangararru a Zariya

0

A ranar Talata ne Hukumar tsaro na ‘Sibul Difens’ NSCDC ta bayyana cewa jami’an ta sun kubutar da mutane 11 dake tsare a wasu gidajen kangararru biyu a Zariya jihar Kaduna.

Kafin hakan mai rikon kujerar gwamnan jihar Kaduna, mataimakiyar gwamnan jihar Hadiza Balarabe ta jagoranci jami’an ‘yan sanda zuwa wani gidan kangararru da ke Rigasa, inda suka kubutar da wasu mutane da mafi yawan su matasa ne har 147.

Gidan jaridar ‘Punch newspapers’ ta rawaito cewa jami’an tsaron NSCDC sun far wa wadannan gidaje biyu a Limanchi Corner da Marmara inda suka iske wadannan mutane masu shekaru 11 zuwa 40 daure cikin ankwa.

Mataimakin kwamandan hukumar Nnegha Onyema ya bayyana cewa uku daga cikin wadannan mutane da ke tsare a wadannan gidaje sun rigamu gidan gaskiya a dalilin azabar da suka sha.

“ Allah ya bamu sa’an cafke shugabanin wadannan gidaje biyar wanda za mu hada su da yaran da muke kubutar mu danka su ga hukumar kare hakkin dan adam domin yanke musu hukunci.

Abdullahi Ishola daya daga cikin wadannan yara da aka kubutar ya bayyana wa manema labarai cewa wani dan uwan sa ne ya kawo shi gidan.

“Ni dalibi ne a kwalejin kimiya da fasaha dake jihar Osun. Wata rana wani dan uwana ya roke ni na raka shi zuwa wani waje inda kafin na ankara kawai sai naga an saka ni cikin ankwa.

“Shugabanin gidan sun azabtar da ni sannan sun hana ni abinci na tsawon kwanaki da dama.

Muktar Aliyu wanda daya daga cikin shugabanin wadannan gidaje yace ya karbi wadannan yara ne da izinin iyayen su sannan ko kadan bai azabtar da su ba.

Mai rikon kujerar gwamnan jihar Kaduna Hadiza Balarabe ta nuna bacin ranta game wannan abu da ake yi wa mutane a wadannan gidaje sannan ta ce gwamnati za ta dau mataki domin hana kafa irin wadannan gidaje a jihar.

Hadiza ta yi kira ga iyaye da su daina kai ‘ya’yan su irin wadannan gidaje cewa duk wadanda aka kama ya kai dansa irin wannan gida zai kuka da kansa.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, ta kubutar da mutane sama da 300 a wani gidan horas da kangararru da ke tsare sama da watanni uku kowanen su.

Yawancin wadanda aka samu a gidan suna daure ne cikin ankwa.

Share.

game da Author