HUKUNCIN KOTUN KOLI: ‘Yan kama-karya sun yi fashin fannin shari’ar Najeriya – Inji Atiku

0

Dan takarar zaben shugabqn kasa na 2019, a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ‘yan kakuduba da gada-gada a karshashin Shugaba Muhammadu Buhari sun kwance zanin da aka rufa asirin fannin shari’a a kasuwa.

Atiku ya yi wannan kakausan lafazi ne a bayanin da ya fitar yau Laraba, kadan bayan da Kotun Koli ya yi watsi da karar da ya daukaka ta hukuncin Kotun Daukaka Kararrakin Zaben Shugaban Kasa, inda ba a ba shi nasara ba.

A jawabin na sa ba yau, Atiku ya ce hukuncin da Kotun Koli ta yanke a yau, ya nuna yadda kama-karya ya samu gindin zama a karkashin mulkin Buhari.

Duk da cewa ya karbi kaddarar hukuncin, amma Atiku ya ce fannin shari’a a karkashin mulkin Buhari ya koma hannun ‘yan gada-gada, ta yadda kimar sa ta zube warwas.

Ya ce tsarin kama-karya da Buhari ke yi a kasar nan, ya zama tsumagiyar kan hanya, hatta ‘yan jarida sai fyadar ‘ya’yan kadanya Buhari ke yi musu, ana garkame su.

Akwai ‘yan jarida da ke kulle wadanda aka tsare a wannan mulki na Buhari, kamar dai irin yadda Buhari ya rika garkame ‘yan jarida a lokacin da ya yi mulkin soja.

Sannan kuma an soki Buhari ganin yadda ya cire Babban Jojin Najeriya ana kusa da zaben 2019, ya maye gurbin sa da Tanko, wanda ya shuhabancin alkalan da suka yi watsi da karar da Atiku ya daukaka a yau Laraba.

Atiku ya ce ‘yan Najeriya dai sun ga abin da Kotun Koli ta aiwatar. Don haka mutunci dai marada ce, idan ya zube kasa shikenan.

Sai dai kuma jam’iyyar APC ta yi na’am da hukuncin da Kotun Koli ta yanke, cewa hakan daidai ne.

A na sa bangaren, Atiku ya ce ba zai daina rajin neman a yi daidai a kasar nan ba. Domin kamar yadda ya ce, idan ba a tashi an gyara kasar nan ba, to kasar za ta iya juyin waina, ta kice da mu baki daya.

Share.

game da Author