Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa duk wani mai hannu a harkallar da aka kulla da kamfanin P&ID da ke neman janyo wa Najeriya mummunar asara, sai an hukunta shi.
A jawabin sa ba yau Talata, Ranar ‘Yanci, Buhari ya ce irin yadda aka kulla makirci da makarkashiyar kwangilar kamfanin P&ID a baya, ya nuna irin mummunar illar da aka yi wa tattalin arzikin kasar nan.
Shugaba Buhari ya ce ba za a zura a kyale wasu tsirarun marasa kishin kasa da jama’ar ta su nemi karya tattalin arzikin kasar nan ba.
Sai ya ce gwamnati na nan na ta kokarin ganin an hukunta masu hannu a cikin harkallar.
Buhari ya kara da cewa gwamnatin sa na nan na hada karfi da Majalisar Tarayya domin samar da dokar hukunta mutumin da ya aikata laifi ko ma a ina ne.
Ya kuma yi kira ga daukacin jihohi da su rika taka-tsantsan wajen kashe kudade. Ya ce duk wata mu’amalar da za a yi, a rika yin ta idp-na-ganin-ido, na kumbiya-kunbiya ba.
A baya, a cikin jawabin na sa, Buhari ya kara jaddada aniyar gwamnatin sa wajen kare lkan iyakokin kasar nan da kuma cikin gida da Yankin Neja Delta.
Sannan kuma ya kara yin gargadin cewa gwamnati ba za ta sassauta wa masu sumogal din kayayyakin da aka haramta shigo da su daga waje ba.
Ya ce sumogal harkar karya tattalin arziki ce, wadda gwamnati ba za ta amince da ita ba.
Discussion about this post