Harin da aka kai wa Oshiomhole ya fusata APC

0

Jam’iyyar APC ta yi Allah-wadai da harin da wasu su ka yi tattaki har gida su ka mai wa Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole.

An kai masa harin ne a ranar Asabar, wanda ana zargin ‘yan bangar siyisa da ‘yan daba ne suka kai masa harin.

Harin da aka kai masa din a gidan sa da ke unguwar Okoroutun, yankin GRA a cikin Benin, a Jihar Edo dai jaridar Punch ta fara ruwaito cewa tsagerun sun rika rera wakar “Oshiomhole barawo”, kafin daga bisani jami’an tsaro su tarwatsa su.

Sai dai kuma a cikin wata sanarwa da kakakin yada labarai na APC, Lanre Issa-Onilu ya fitar jiya Lahadi da yamma, ya yi tir da harin tare da bayyana shi da cewa hari ne aka kai da nufin kashe shugaban jam’iyyar APC.

Ya ce jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro na ci gaba da bincike.

“Duk da cewa Shugaban Jam’iyyar APC, ya yi kira da a kwantar da hankali bayan harin neman kashe shi da wasu suka kai masa, mu na kira ga Shugaban ‘Yan Sanda na Kasa da sauran jami’an tsaro su bincika wannan al’amari domin hukunta wadanda suka dauki nauyin kai hari da kuma wadanda su ka kai harin.

“Hakan na nuni da cewa wadanda suka dauki nauyin kai wannan harin na kokarin haifar da rikici a jihar Edo, saboda wani muradi na siyasa na su, wanda zai kawo barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a. Ran dan Adam ya fi daraja a kan muradin siyasar ko wane ne”. Inji shi.

Share.

game da Author